Jam’iyyar APC ta fi PDP tabarbarewa Inji Segun Oni
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni, wanda ya sauya-sheka kwanan nan, ya yi wata hira da ‘Yan jarida, inda ya yi magana game da siyasar kasa, tafiyar jam’iyyar APC da kuma PDP.
Segun Oni ya bayyana cewa kotu da aka kai shi a lokacin ya na rike da jam’iyyar PDP a Kudancin Najeriya, ya na cikin mafararsa komawa APC. Sai dai a nan ma, Oni bai samu abin nema ba.
Oni ya bayyana cewa ba zai iya kawo ko da mutane 10 daga cikin ‘yan gidansa a siyasa da su ka amfana da gwamnatin APC ba. A cewarsa, ko kujerar Kansiloli ba a ba na-kusa da shi a APC.
Cif Segun Oni ya ke cewa duk da yadda abubuwa su ka kasance bai yi da-na-sanin taimakawa APC wajen tika PDP da kasa a zaben Ekiti ba, domin a lokacin APC ya ke yi wa aiki a jihar.
A zaben Ekiti, Segun Oni ya hada kai da Kayode Fayemi wanda ya tika shi da kasa a lokacin ya na gwamna. A cewarsa, babu abin da ke tsakaninsa da gwamna Fayemi sai Allah-sa-alheri.
Sai dai ‘Dan siyasar ya ce sabaninsa da gwamnatin APC a Ekiti shi ne rashin damawa da su. ya ce a wani taro da ya yi da Magoya bayansa 250, babu wanda ya ce ya karu da gwamnatin APC.
KU KARANTA: Ardo: Zai yi wa PDP kyau ta tsaida Sanusi takarar Shugaban kasa a 2023
Ya ce: “Mun nemi mu yi takara, sun karbe mani kudi, sun hana mu takara, sun ki maido mana kudinmu. Ta ya za ka gamsar da mutum irin wannan ya cigaba da zama a jam’iyyar nan?”
Da ya ke kokawa da tsarin APC mai mulki, Oni ya ce a lokacin da ya ke gwamna a PDP, bai taba sa baki game da zaben shugabannnin jam’iyya a Mazabu ba, akasin abin da ya ce ake yi a yau.
Jagoran na APC a lokacin baya ya ce a lokacin da aka kafa gwamnati a Ekiti, ya sa burin cewa Masoyansa za su san ana yi. A karshe sai ga shi Magoya bayan na sa sun kare a gaban kotu.
Da aka tambayesa ko ya kai kuka wajen shugabanni jam’iyya; Bola Tinubu da Adams Oshiomhole game da abin da aka yi wa na kusa da shi, sai ya ce ya yi, amma ba a dauki mataki ba.
Cif Oni ya ce ba tare da jin tsoron kowa ba, PDP ya fi APC. A cewarsa a APC ba a mutunta tsarin dokan cikin gida, sannan kuma ya ce shugabannin PDP sun fi sanin darajar ‘Yan siyasa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng