An sake samun bullar cutar coronavirus a wata jahar Najeriya

An sake samun bullar cutar coronavirus a wata jahar Najeriya

Rahotanni sun kawo cewa jahar Oyo ta samu mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus, inda hakan ya zama lamari na 23 da aka samu a Najeriya.

Akwai wadanda suka kamu mutum 16 a Lagas; daya a Ekiti; biyu a Ogun sannan uku a babbar birnin tarayya Abuja.

A wani jawabi da aka saki a safiyar ranar Lahadi, Seyi Makinde, gwamnan Oyo, ya ce jami’an hukumar lafiya a jahar suna hada kai da asibitin jami’ar jahar da tawagar Ibadan kan lamarin.

Gwamnan ya kara da cewa an killace wani da ya dawo daga kasar Amurka kwanan nan.

An sake samun bullar cutar coronavirus a wata jahar Najeriya
An sake samun bullar cutar coronavirus a wata jahar Najeriya
Asali: Twitter

“Gwajin COVID-19 da aka yi wa wani a Bodija ya dawo cewa yana dauke da cutar. An saki sakamakon gwajin da misalin karfe 5:35 na yammacin ranar Asabar, 21 ga watan Maris,” in ji shi.

Gwamnan ya saki jerin layukan da za a kira domin agaji kamar haka: 08038210122/ 08023228267/ 08073431342.

Hakan na zuwa ne kwanaki uku bayan an gudanar da gagarumin gangami na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Ibadan, babbar birnin jahar.

KU KARANTA KUMA: Kaduna ta hana manyan tarurruka da harkokin addinai da bukukuwan jama’a

Biyo bayan sukar taron da aka yi, sai Makinde ya bayar da hakuri cewa bai kamata ayi irin wannan taron ba a daidai wannan lokacin da duniya ke yakar annoba.

A wani labarin kuma mun ji cewa Jama'ar Daura da ke jihar Katsina a ranar Asabar sun fada addu'o'i don neman kariya daga sabuwar mugunyar cutar coronavirus.

Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq, ya jagoranci mazauna garin sallah ta musamman don rokon Ubangiji kariya daga cutar. Sarkin mai shekaru 84 ya ja sallar ne a farfajiyar fadarsa.

Ya bukaci mazauna garin da su kalla muguwar cutar da wata jarabawa daga Allah.

Yayi kira ga jama'a da su tsananta addu'ar neman kariya daga cutar da sauran cutukan da ke kashe jama'a.

Sarkin ya kwatanta wannan cutar da hatsarin da yafi na Boko Haram, ya kuma yi addu'ar cewa Ubangiji ya kawo karshen wannan masifa da gaggawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel