Al’ummar jahar Kano sun yi maraba da rage farashin mai da Buhari ya yi

Al’ummar jahar Kano sun yi maraba da rage farashin mai da Buhari ya yi

Al’ummar jahar Kano, musamman matuka motoci sun bayyana farin cikinsu biyo bayan matakin karya farashin man fetir da gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito gwamnatin Najeriya ta sanar a ranar Laraba cewa ta rage farashin litan man fetir daga 145 zuwa 125, hakan ya faru ne sakamakon karyewar farashin gangan danyen mai a kasuwannin duniya a dalilin yaduwar annobar Coronavirus.

KU KARANTA: Hatsari ba sai a mota ba: Rijiya ta kashe mutane 2, ta jikkata jami’in kwana-kwana

Direbobi da dama da suka tattauna da majiyar Legit.ng sun bayyana farin cikinsu, daga cikinsu akwai Malam Abdulkarim Sarki matukin Keke Napep, wanda ya ce ya yi farin cikin da wannan cigaba saboda hakan zai rage masa kudin da yake kashewa wajen shan mai.

“Na sayi mai a yau, kuma na samu ragin N700 ba kamar yadda na saba kashewa a baya kafin rage farashin man ba.” Inji shi. Haka ma Kamalu Abubakar ya jinjina ma gidajen mai da ta yadda suka gaggauta rage farashin man.

Shi kuwa Malam Mustapha Bello kira ya yi ga gwamnati da ta tabbata ta sanya idanu a kan gidajen man da zasu rage farashin man ba, saboda a cewarsa bai kamata rijiya ta bayar da ruwa ba, amma guga ta hana.

A wani labarin kuma, masu iya magana su kan ce wai ‘Hatsari ba sai a mota ba’ wasu mutane biyu sun gamu da ajalinsu sakamakon tsautsayi da ya shigar dasu cikin wata tsohuwar rijiya a kauyen K-Vom dake cikin karamar hukumar Jos ta kudu a jahar Filato.

Mutanen biyu sun gamu da hatsarin ne a lokacin da suke aiki a cikin rijiyar, inda suka zurma cikin wani kogo dake cikin rijiyar, daga nan jama’an yankin suka kira Yansanda, wanda su kuma suka kira jami’an hukumar kwana kwana don bayar da agaji.

Sai dai a kokarin wani jami’in hukumar kwana kwana na ceto mutanen ta hanyar janyo su waje, shi kansa da kyar ya tsallake rijiya da baya, amma duk da haka sai da ya samu rauni babba a kan sa, inji majiyar Legit.ng.

Shugaban hukumar kwana-kwana ta jahar Filato, Mista Samuel Nzwak ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace: “Abinda ya faru shi ne wasu Yansanda sun shiga ofishinmu a Bukuru da safe suka nemi mu kai ma wasu mutane biyu dauki da suka fada cikin rijiya a K-Vom.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel