Rundunar 'yan sanda ta damke ma'auratan da ke taimaka wa masu garkuwa da mutane

Rundunar 'yan sanda ta damke ma'auratan da ke taimaka wa masu garkuwa da mutane

Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta damke wasu ma'aurata da ake zargi da taimakawa masu garkuwa da mutane a yankin Ogori/Magongo da ke Kogi ta tsakiya.

Kakakin rundunar 'yan sanda jihar, Willaim Aya ya sanar da manema labarai a ranar Juma'a a garin Lokoja, cewa ma'auratan na yi wa masu garkuwa da mutanen girki a maboyarsu da ke daji.

Wasu majiyoyi da ba a tabbatar ba sun ce a kalla mutane shida aka yi garkuwa dasu a kan hanyar Ageva/Ogori tsakanin ranar 12 ga watan Maris zuwa ranar Laraba da ta gabata.

An gano cewa masu garkuwa da mutane sun sauya wajen zama zuwa Okene, Ogori/ Magongogo da kuma yankin Ageva/Ogori a makonni biyu da suka gabata.

Wannan ya biyo bayan ruwan wutar da aka yi wa 'yan ta'addan a yankunan Kogi ta yamma da Kogi ta gabas a makonni biyu da suka gabata.

Wata majiya ta sanar da manema labarai cewa an sace wata mata da diyarta a kan babbar hanyar Akpafa Magongo a ranar 12 ga watan Maris.

Wadanda aka sace din sun hau mota ne a kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Akpafa. "A ranar Juma'a 12 ga watan Maris, masu garkuwa da mutane sun sace wasu matafiya a kan hanyarsu ta zuwa Magongo-Okene inda suka tsallaka dasu zuwa sansaninsu da ake zargi yana titin Ogori."

Rundunar 'yan sanda ta damke ma'auratan da ke taimaka wa masu garkuwa da mutane

Rundunar 'yan sanda ta damke ma'auratan da ke taimaka wa masu garkuwa da mutane
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda takalma suka tona wa wasu 'yan fashi da makami asiri a Zaria

"A ranar Talata 17 ga wata, an sace wani mutum wanda ake kira da Anchorman a kan hanyar shi ta zuwa Ogori daga Okene a kan babur dinsa. Bayan sun kai sansaninsu da shi, sai ya hadu da wani wanda aka sace tare da wani mutum mai suna Woli Apara," ya ce.

Daga baya sai wadanda aka sace din suka tsere da kansu. Kafin hankulansu su koma jikinsu ne masu garkuwa da mutanen suka kara kai hari a da karfe biyar na yamma. Sun sace wani Toyin mai gidan ruwa.

Aya ya bayyana cewa an tura rundunar hadin guiwa ta sojoji da 'yan sintiri zuwa yankin inda suka yi nasarar ceto wadanda aka sace din. An kuma kama Woli Apara da matarsa a tare dasu sannan suna samar da muhimman bayanai ga 'yan sandan.

Kamar yadda jaridar The nation ta bayyana, matan yankin sun fara addu'a don samun sassauci daga ibtila'in garkuwa da mutane da ya addabi yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel