Dino Melaye ya bayyana ainahin abinda zai yi maganin cutar Corona a duniya

Dino Melaye ya bayyana ainahin abinda zai yi maganin cutar Corona a duniya

Tsohon Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta Yamma, Dino Melaye yayi magana akan sabuwar cuta mai kisa da ta addabi duniya wato cutar Coronavirus, wacce aka fi sani da COVID-19

Tsohon Sanatan yayi wannan bayani ne a shafinsa na Twitter inda ya ce maganin cutar ba wai sanya abin rufe hanci ko wanke hannu ba ne, hanya daya ita ce mutane su koma ga Allah.

Bayan ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter Dino Melaye ya kawo wata aya a cikin littafin Bibble ya sanya hotonta a shafin nasa.

"Lokacin dana kulle sararin samaniya don kada ruwan sama ya sauka, ko kuma na aikowa da al'umma cuta.

KU KARANTA: Budurwa dauke da tsohon ciki ta sha guba bayan ta gano cewa saurayinta yana da aure

"Idan har mutane da suke bauta mini za su dawo gareni suyi addu'a sannan kuma su nemi gafarata akan abubuwan da suka yi na ba daidai ba, ni kuma zan jikansu na yafe musu na kuma cire musu wannan masifa dana aiko musu.

"Yanzu idanuna a bude suke, kuma kunnuwana suna jin duk addu'o'inku," a rubutun da tsohon sanatan ya wallafa.

Ga dai hoton shafin littafin Bibledin da ya wallafa.

Dino Melaye ya bayyana ainahin abinda zai yi maganin cutar Corona a duniya

Dino Melaye ya bayyana ainahin abinda zai yi maganin cutar Corona a duniya
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel