Kaduna ta hana manyan tarurruka da harkokin addinai da bukukuwan jama’a

Kaduna ta hana manyan tarurruka da harkokin addinai da bukukuwan jama’a

Daga cikin matakan kare al’umma daga kamuwa da yada annobar coronavirus, gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da hana tarukan addini da manyan tarurruka a jahar.

“Kamar yadda babu lamari na coronavirus a jahar zuwa yanzu, gwamnati na da alhakin aiki tare da shugabanninmu da mazauna jaharmu domin tabbatar da ganin ba a samu barkewar cutar da yada ta ba a jahar,” cewar sanarwar.

A wani jawabi daga Sir Kashim Ibrahim ya bayyana cewa an shawarci limamai da kada su yi sallar Juma’a a yau.

A kan haka gwamnati na bi shawarar kasar Saudiyya, wacce take cibiyar musulunci wajen dakatar da sallah a tsarkakan masallatai biyu a Makkah da Madina.

A kasashe da dama kamar su Saudiyya, Kuwait da tarayyar laraba an karfafa wa jama’a gwiwar yin sallah a gida kuma ba a jam’i ba kamar yadda aka saba.

Kaduna ta hana manyan tarurruka da harkokin addinai da bukukuwan jama’a
Kaduna ta hana manyan tarurruka da harkokin addinai da bukukuwan jama’a
Asali: Facebook

Don haka gwamnatin Kaduna ta umurci dakatar da yin khamsa-salawat a jam’i har zuw lokacin da lamarin Coronavirus zai lafa.

Jawabin ya kuma umurci kiristoci da su dakatar da taro a cocina.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: An dakatad da Khamsu-Salawati a Masallacin Harami da na Annabi (SAW) dake Madina

Ta kuma bayyana cewa ana iya gudanar da sauran lamuran addinai a tsakanin mutane da ba su wuce 10 ba, Sannan kuma an haramta duk wani taro da zai kai na mutum 50 a jahar har sai yadda hali ya yi.

Tuni dai gwamnatin jahar ta sanar da rufe makarantu a jahar daga ranar Litinin mai zuwa.

A wani labari na daban, mun ji cewa Wata tsohuwa mai shekara 103 a kasar Iran ta warke bayan ta kamu da sabuwar cutar coronavirus, duk da hujjar da ya nuna cewa tsofaffi sun fi kasancewa cikin hatsarin kamuwa da annobar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An kwantar da matar wacce ba a bayyana sunanta ba a asibitin da ke tsakiyar birnin Semnan kusan tsawon mako guda.

Amma daga bisani aka sallame ta bayan ta warke ta samu lafiya, kamar yadda aka rahoto Shugaban sashin kimiyar likitoci na jami’ar Semnan, Navid Danayi yana fadi a ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel