Tsohuwa yar shekara 103 ta warke daga cutar coronavirus a Iran

Tsohuwa yar shekara 103 ta warke daga cutar coronavirus a Iran

Wata tsohuwa mai shekara 103 a kasar Iran ta warke bayan ta kamu da sabuwar cutar coronavirus, duk da hujjar da ya nuna cewa tsofaffi sun fi kasancewa cikin hatsarin kamuwa da annobar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An kwantar da matar wacce ba a bayyana sunanta ba a asibitin da ke tsakiyar birnin Semnan kusan tsawon mako guda.

Amma daga bisani aka sallame ta bayan ta warke ta samu lafiya, kamar yadda aka rahoto Shugaban sashin kimiyar likitoci na jami’ar Semnan, Navid Danayi yana fadi a ranar Talata.

Matar ita ce mutum na biyu da ta warke daga cutar cikin tsoffi a Iran.

Tsohuwa yar shekara 103 ta warke daga cutar coronavirus a Iran

Tsohuwa yar shekara 103 ta warke daga cutar coronavirus a Iran
Source: Facebook

Dayan mutumin da ya warke shine wani dan shekara 91 daga Kerman, a kudu maso gabashin Iran, kamar yadda majiyar Legit.ng ta rahoto.

Bayan ya yi fama da rashin lafiya na kwanaki uku, sai ya warke a ranar Litinin duk da cewar yana da wasu rashin lafiya da suka hada da hawan jini da asthma.

Rahoton bai bayyana yadda aka yi tsaffin biyu suka warke ba.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus ba sabon abu ba ne - Sheikh Aminu Daurawa

A wani labari na daban, mun ji cewa Masarautar Saudiyya ta hana shiga Masallatai biyu masu daraja na Makkah da Madina, fari daga ranar Juma'a, 20 ga Maris ga masu khamsu-Salawati cikin matakan da gwamnatin kasar ke dauka wajen takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Kakakin ma'aikatar kula da lamarin Masallacin Harami da Annabi SAW dake Madina ya sanar da hakan ne ranar Juma'a. A yanzu, mazauna cikin Masallacin da ma'aikata kadai suka sallaci sallar Asuba a yau Juma'a.

Yace: "Hukumomin tsaro da kiwon lafiya sun yanke shawarar hana mutane shiga cikin Masallacin Harami da na Annabi dake Madina fari daga ranar Juma'a 20 ga Maris."

"Hakan yana cikin matakan da kiyaye cigaba da yaduwar cutar Coronavirus."

Ma'aikatar Lafiyan kasar Saudiyya ta tabbatar da cewa kawo ranar Alhamis, mutane 274 sun kamu da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel