Adam A Zango yayi bayani akan alakarsa da jaruma Rahama Sadau

Adam A Zango yayi bayani akan alakarsa da jaruma Rahama Sadau

- Bayan maganganun da mutane suka yi tayi a shafukan sadarwa game da hotunan Adam A Zango da Rahama Sadau da suka fita

- Jarumin ya fito fili yayi magana akan ainahin alakar dake tsakaninsa da jarumar

- Mutane dai na ganin cewa akwai alamun soyayya tsakaninsa da jarumar musamman ma ganin wadannan hotuna da suka dauka

A cikin makon nan mafiya yawancin masu bibiyar shafukan sada zumunta na 'yan fim da na labarai da sauran su kama daga Facebook, Instagram zuwa ga Whatsapp sunyi ta tozali da wasu hotuna na jarumi Adam A Zango da jaruma Rahama Sadau cikin wani yanayi da ya dauki hankula matuka.

Hotunan dai sun nuna kusanci sosai tsakanin jaruman inda har wasu ke zaton ko soyayya suke wasu ma har suna fatan alkhairi wasu na cewa sun dace da sauran su.

Adam A Zango yayi bayani akan alakarsa da jaruma Rahama Sadau
Adam A Zango yayi bayani akan alakarsa da jaruma Rahama Sadau
Asali: Facebook

Sai dai ganin yadda ake ta cece kuce kan hotunan yasa jarumin shima ya wallafa wasu daga cikin hotunan a shafinsa kana ya bayyana matsayin Rahama Sadau a wajensa, inda a farko ya rubuta cikin harshen turanci cewa:

KU KARANTA: Hotuna: Alaka mai karfin gaske na kulluwa tsakanin Rahama Sadau da Adam A Zango

"Aboki na kwarai shine wanda zai zo gareka a yayin da duniya ta guje ka!! Na gode Rahama Sadau da zama abokiya ta!!

Kana ya kara wallafa wani rubutun yace: "Aboki daya mai halacci yafi abokai dubu na bogi, Rahama Sadau tana yi mini hallaci dan haka nima ta saurari sakayyata."

Wannan ya isa ya sharewa masu zaton soyayya tsakanin jaruman tantama su san zallar shakuwa ce da aminci ta kai su ga samun kusancin da har ake tsammanin wani abun daban.

Kamar yadda kuka sani jarumin ya sha fama da abokai da makusantan sa wanda har ta kai ga jarumin yayi furuci na cewa ba zai sake yin aboki na kut da kut ba, amma ga dukkan alamu Rahama Sadau ta fita zakka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel