Corona: Buhari ya yi raddi ga Sanatoci bayan sun nemi ya fito ya ma yan Najeriya jawabi

Corona: Buhari ya yi raddi ga Sanatoci bayan sun nemi ya fito ya ma yan Najeriya jawabi

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga majalisar dattawa biyo bayan neman da ta yi na shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya yi ma yan Najeriya jawabi game da annobar cutar Coronavirus tare da kokarin da gwamnatinsa take yi ko hankulan jama’a zai kwanta.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana kiran da majalisar ta yi a matsayin kokarin bata ma shugaban kasa suna da kuma siyasantar da maganan, inda yace ya kamata yan majalisar su sani cewa yanzu ba lokacin neman suna bane.

KU KARANTA: Annobar Corona: Jerin Jahohi 13 a Najeriya da suka rufe makarantu tare da hana taron jama’a

“Neman sunan da wasu manyan yan majalisar dattawa suka yi na cewa wai shugaban kasa na nuna halin ko in kula ga halin da ake ciki kawai saboda bai yi ma yan Najeriya jawabi ta talabijinba wata hanya ce na siaysantar da maganan.

“Kamata yayi Arewa, kudi, yamma da gabas su hadu kai wajen yaki da wannan annobar ba tare da la’akari da bambance bambancen dake tsakaninsu ba, muna kira ga yan Najeriya kada su dauki wannan matsala a matsayin wata daman a nuna adawa ga gwamnatin APC.” Inji shi.

Shehu ya bayyana wasu daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka wajen shawo kan yaduwar cutar da suka hada da hana tafiye tafiye ta tashoshin jiragen sama, rage farashin mai da sauransu.

Daga karshe Shehu ya tabbatar ma yan Najeriya cewa a shirye suke wajen maganin yaduwar Coronavirus, don haka babu bukatar tsoro ko fargaba, kuma zuwa yanzu duk matakan da gwamnatin ta dauka suna haifar da da mai ido.

“Shugaban kasa ya aminta da ministocinsa da ya baiwa aikin tabbatar da yaki da yaduwar cutar, haka zalika ya aminta da hukumar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya duba da kokarin da take yi, kuma zamu cigaba da sanar da yan Najeriya halin da ake ciki.

“Sa’annan muna fatan yan Najeriya za su bi duk umarni da sharuddan da aka gindaya musu don samun nasarar kawar da wannan cuta.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel