A gaban Uban da ya haifeni ma na sha shisha ballantana a gabanku - Martanin Tumba Gwaska ga masu zaginta

A gaban Uban da ya haifeni ma na sha shisha ballantana a gabanku - Martanin Tumba Gwaska ga masu zaginta

- Jaruma Tumba Gwaska ta mayarwa da mabiyanta da suka yi caa a kanta martani kan wani bidiyo da ta saki

- Jarumar dai ta saki bidiyon ne tana shan shisha, hakan ya sanya da yawa daga cikin mabiyanta suka fara zaginta

- Ta bayyana cewa a gaban mahaifin da ya haifeta ma tasha shisha ballantana kuma a gaban wasu

Ga dukkan alamu mabiyan jaruma Tumba Gwaska sun kaita makurar bacin rai wanda har ta kai ga ta wallafa wani bidiyo tana musu martani kan cece-kucen da suke akan ta kan tayi bidiyo tana shan shisha.

Cikin fushi jarumar ta wallafa wani bidiyo, inda take martani ga masu zargin ta kan sun ganta da shisha, ta bayyana musu cewa tsarin rayuwar ta daban da tasu kuma ita 'yar Niger ce, 'yar Faransa, dan tana shan shisha zata yi bidiyo ba ta ga dalilin da zai sa ta ajiye shishar ba tunda ta sha a gaban mahaifinta ma balle wasu.

Jarumar ta kara da cewa ita ba 'yar kwaya bace shisha ce kawai take sha kuma ta nunawa duniya kuma duk wanda ya zage ta sai ta rama tunda uwa bata fi uwa ba, kuma tana daukar sunan masu zagin nata zasu san ko ita wacece zata dauki mataki.

KU KARANTA: Daga gadi na fara amma yanzu yanzu na mallaki kamfanin hakar man fetur da iskar gas - AD Patrick

Jaruman dai sunyi kaurin suna wajen jawo kace-nace a kafafen sadarwa akan abubuwan da suke yi.

A kwanakin baya aka sha fama da badakalar fitattun jarumai guda biyu na Kannywood, wato jaruma Maryam Booth da kuma jaruma Safara''u ta cikin shirin 'Kwana Casa'in', wadanda bidiyonsu na tsiraici ya dinga yawo a kafafen sadarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel