IPPIS: Shugabannin Jami’a sun karbi N58, 000 a matsayin albashinsu – ASUU

IPPIS: Shugabannin Jami’a sun karbi N58, 000 a matsayin albashinsu – ASUU

Kungiyar ASUU ta Malaman jami’o’in Najeriya ta ce ‘Ya ‘yanta da su ka yi taurin kai, su ka jefa kansu cikin tsarin IPPIS su na da-nasin aikin da su ka yi a yanzu.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, ASUU ta nuna ba ta yi nadamar kin shiga tsarin albashin IPPIS ba saboda abin da wasu ke gani daga baya.

A cewar shugaban kungiyar ASUU na Yankin Legas, akwai Farfesohin da aka biya N55, 000 rak a matsayin albashinsu na Watan Fubrairu bayan sun yi rajista da IPPIS.

Farfesa Olusiji Sowande ya bayyana cewa haka zalika akwai shugabannin jami’o’in da N58, 000 kacal su ka samu a matsayin albashinsu na watan daga tsarin IPPIS.

Rahotan ya na cewa Olusiji Sowande ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya zanta da Manema labarai a Jami’ar Tai Solarin da ke Ijagun, Garin Ijebu-Ode a jihar Ogun.

KU KARANTA: Dangote da manyan kasa sun halarci daurin auren Yaran IGP

IPPIS: Shugabannin Jami’a sun karbi N58, 000 a matsayin albashinsu – ASUU
ASUU ta ce Gwamnati ta biya Farfesohin da ke karbar makudan kudi N55, 000
Asali: Twitter

ASUU ta na zargin tsarin da gwamnati ta kawo na biyan albashi da lakume kudin ma’aikata. Manyan jami’o’in da ke da makudan albashi sun kare da karbar kudi kadan.

Farfesan ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ke tare da sauran shugabannin ASUU na reshe da jami’an kungiyar na shiyyar. Sowande ya ce akwai badakalar a tsarin.

Olusiji Sowande ya zargi gwamnatin Buhari da cin bashin kudi har fam Dala miliyan 140 domin horas da ma’aikata a kan yadda za su rika aiki da manhajar ta IPPIS.

Shugaban kungiyar ya karyata rade-radin cewa Malaman jami’a rututu sun shiga tsarin, sannan ya bayyana cewa barazanar rashin biyan albashi ba zai yi aiki a kansu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng