Da dumi-dumi: Sakamakon gwaji ya nuna wanda ake zargi da coronavirus a Katsina bai da cutar

Da dumi-dumi: Sakamakon gwaji ya nuna wanda ake zargi da coronavirus a Katsina bai da cutar

Ma’aikatar lafiya ta jahar Katsina ta sanar da cewar sakamakon gwajin da aka yi wa wanda ake zargin yana dauke da cutar coronavirus a jahar ya nuna baya dauke da cutar.

A ranar Laraba, 18 ga watan Maris ne gwamnatin jahar Katsina ta sanar da mutum na farko da ake zargin yana dauke da cutar ta coronavirus, sannan ta yi alkawarin sanar da jama’a sakamakon gwajin da aka yi masa a yau Alhamis, 19 ga watan Maris.

Mutumin wanda ya killace kansa, ya dawo ne daga kasar Malaysia sannan ya fara jin wasu alamu da ke bukatar bincike.

Da yake jawabi ga manema labarai a safiyar yau Alhamis, kwamishinan lafiya na jahar, Injiniya Yakubu Danja, ya ce sakamakon gwajin ya nuna baya dauke da ita, inda ya kara da cewa babu lamari na cutar da aka tabbatar a Katsina a yanzu haka.

Da dumi-dumi: Sakamakon gwaji ya nuna wanda ake zargi da coronavirus a Katsina bai da cutar
Da dumi-dumi: Sakamakon gwaji ya nuna wanda ake zargi da coronavirus a Katsina bai da cutar
Asali: UGC

Ya shawarci mazauna jahar da su kwantar da hankalinsu sannan su yawaita bibiyar Karin bayanai a kan cutar.

Danja ya kuma yi kira gare su da su daina watsa bayanai da ba a tabbatar ba, musamman ta shafukan soshiyal midiya game da cutar.

Yayinda ya ke kira ga mutane da su kula da tsaftar jiki da na muhalli, ya bukace su da su: “yi amfani da abun wanke hannu mai barasa, da kuma guje ma taro na jama’a sai dai da dalili mai karfi.”

Ya basu tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da yin duk abunda ya kamata domin kare lafiyarsu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Neja ta yi umurnin rufe dukkanin makarantu a fadin jahar saboda coronavirus

A baya mun ji cewa Gwamnonin yankin Arewa maso yamma sun sanar da cewa za a rufe dukkan makarantu da ke yankin na tsawon kwanaki 30 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cikin sakon bayan taro da gwamnonin suka fitar ta bakin shugaban kungiyar gwamnonin yankin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, sun ce ya zama dole a dauki matakin hakan domin kare yaduwar cutar da Coronavirus a yankin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel