Coronavirus ta sa 'Yan Majalisa sun dakatar da zaman jin na bakin al'umma

Coronavirus ta sa 'Yan Majalisa sun dakatar da zaman jin na bakin al'umma

- Majalisar dattawan Najeriya ta dauki wasu matakai na hana yaduwar annobar cutar coronavirus

- A yanzu haka ta dauki matakin dakatar da zaman jin na bakin alúmma da hana baki shiga zauren muhawara

- Shugaban majalisar dattawan Ahmad Lawan ne ya sanar da hakan inda ya ce matakin zai fara aiki ne daga ranar Talata mai zuwa

Majalisar dattawan Najeriya a ranar Alhamis, 19 ga watan Maris, ta dauki wasu matakai na hana yaduwar annobar cutar coronavirus da ta game kasashen duniya.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da fara zaman majalisa ya sanar da dakatar da da zaman jin na bakin alúmma da hana baki shiga zauren muhawara.

Coronavirus ta sa 'Yan Majalisa sun dakatar da sauraron 'muhawara'
Coronavirus ta sa 'Yan Majalisa sun dakatar da sauraron 'muhawara'
Asali: UGC

Ya bayyana cewa wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar Talata mai zuwa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta hana baki daga wasu kasashen duniya shigowa kasar saboda annobar ta cornavirus.

Da farko dai mun ji cewa Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya yi ma yan Najeriya bayani game da bullar annobar cutar Coronavirus, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar ta yanke wannan shawara ne bayan wata doguwar muhawara a zauren majalisar a ranar Laraba, inda ta nemi gwamnatin Najeriya ta dauki kwararn matakai domin kare yaduwar cutar a Najeriya.

Sanata Danjuma Goje na jahar Gombe ne ya gabatar da wannan kuduri a gaban majalisar, inda yace akwai bukatar gwamnatin tarayya, gwamnatin jahohi da gwamnatocin kananan hukumomi su sanya idanu kamar yadda hukumomin kiwon lafiya suka tanada.

“Majalisa ta yi kira ga shugaban kasa ya fito ya yi ma yan Najeriya bayani game da wannan matsalar, manyan kasashen duniya sun yi haka, idan ya fito yayi jawabi ga yan Najeriya, sai an fi daukan maganan da muhimmanci.

“Ba wai mun ce babu abinda take yi bane, amma akwai bukatar gwamnati ta dauki kwararan matakai kamar su hana tafiye tafiye, hana wasu kasashe shigowa kasa, rufe iyakokin kasar, rage taruwar jama’a, tsaurara binciken masu shigowa kasa da kuma killacesu tsawon makonni biyu.

“Haka zalika akwai bukatar majalisar ta baiwa gwamnatin Najeriya dukkanin goyon bayan da take bukata don yaki da cutar, a bude cibiyoyin gwaje gwaje, a hana kamfanonin jiragen sama na kasashen waje tashi daga Najeriya, a kulle filayen sauka da tashin jiragen Najeriya banda Abuja da Legas.”Inji shi.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Kungiyar Ansaruddeen ta dakatar da Sallar Juma'a a masallatanta da ke fadin Najeriya

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel