Tattalin arziki: COVID-19 za ta taba abin abin yin miliyoyin mutane - ILO

Tattalin arziki: COVID-19 za ta taba abin abin yin miliyoyin mutane - ILO

Darekta Janar na kungiyar ‘Yan kwadago ta Duniya, ILO, ya ce kusan mutane miliyan 25 ne za su rasu abin yi a fadin Duniya a sakamakon barkewar cutar COVID-19.

Mista Guy Ryder ya tabbatar da wannan a wani jawabi da ya fitar a babban birnin tarayya Abuja jiya inda ya bayyana sakamakon wani bincike da kungiyar ILO ta yi.

Ya ce: “Binciken da aka yi game da tasirin cutar COVID-19 a kasashen Duniya ya nuna cewa illarsa za ta yi kamari, za ta sa miliyoyin mutane su zama ba su da aikin yi.”

A cewar Guy Ryder: “Matsalar rashin aikin yi da tattalin arzikin da cutar COVID-19 za ta jawo zai iya kara yawan marasa aikin yi a Duniya da mutane har miliyan 25”

“Amma duk da haka, idan aka fito da tsare-tsare na magance annobar kamar yadda aka yi a lokacin da aka shiga matsalar tattalin arzikin 2008, abin zai yi sauki.”

KU KARANTA: Gwamnatin Ogun ta rufe wuraren rawa, cin abinci da wasanni

Tattalin arziki: COVID-19 za ta taba abin abin yin miliyoyin mutane - ILO
Annobar COVID-19 za ta taba masu kananan da matsakaitan ayyuka
Asali: UGC

Wannan bincike da kungiyar ta yi, ya bukaci hukumomi da gwamnatoci na Duniya su maida karfi wajen tsare ma’aikata a wuraren aikinsu, da zaburar da tattalin arziki.

Haka zalika kungiyar ta bukaci masu iko su taimakawa ayyuka da sana’o’in jama’a a wannnan lokaci ta hanyar bada tallafi, hutu, da kuma bada kananan jarin kasuwanci.

A cewar Guy Ryder: “Wannan lamari ya tashi daga matsalar kiwon lafiya, ya zama babban matsalar tattalin arziki da abin yi, wanda ya ke da tasiri ga rayuwar mutane.”

“Mu na bukatar irin abin da ya faru a 2008 a halin yanzu, inda a lokacin Duniya ta maida hankali ta fuskanci matsalar tattalin arziki.” Hukumar NAN ta rahoto wannan dazu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng