An sake samun wani da ake zargin yana da cutar coronavirus a jahar Ondo

An sake samun wani da ake zargin yana da cutar coronavirus a jahar Ondo

Gwamnatin jahar Ondo ta tabbatar da cewar akwai wani da ake zargin yana dauke da cutar Coronavirus a Akure, babbar birnin jahar, inda ake kan kula dashi a yanzu haka.

Rahotanni a ranar Laraba, 18 ga watan Maris, ya nuna cewa an dauki wani mutum mai suna David, wanda ya shigo Najeriya daga Maryland, kasar Amurka a wani asibitin gwamnati a jahar Ondo bayan an yi zargin yana da Coronavirus.

A cewar rahoton, a yanzu haka ana kan kula da mutumin a sashin hatsari da taimakon gaggawa a asibitin koyarwa na Akure, babbar birnin jahar.

An sake samun wani da ake zargin yana da cutar coronavirus a jahar Ondo
An sake samun wani da ake zargin yana da cutar coronavirus a jahar Ondo
Asali: Twitter

Da yake tabbatar da rahoton, kwamishinan lafiya, Dr Wahab Adegbenro ya bukaci mutanen jahar Ondo da su kwantar da hankalinsu domin lamarin na karkashin kulawa, Channels TV ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya biyu, mai jego da jaririnta sun kamu da cutar Coronavirus

A wani labarin kuma, mun ji cewa an samu mutumin farko da ya kamu da cutar coronavirus a Jihar Ekiti da ke Kudancin Najeriya a Ranar Larabar nan, 18 ga Watan Maris, 2020.

Kwamishinar lafiya ta Ekiti, Dr. Mojisola Yaya-Kolade, ta nuna cewa wani Direban mota da kwanaki ya tuka wani Mutumin Amurka ya kamu da cutar a halin yanzu. Kawo yanzu dai ainihin wannan Bawan Allah da ya zo daga Amurka ya rasu.

Ana zargin cewa wanda ya tuka shi daga Garin Ibadan zuwa Ekiti ya dauki cutar a wurinsa.

Gwamnatin Ekiti ta tabbatar da wannan labari mara dadi ne a daren Ranar Laraba. Kwamitin da aka kafa domin yaki da cutar #COVID-19 a jihar ya bayyana haka a jiya.

A cewar Kwamishinar lafiyar, wannan Direban da ya kamu da cutar ya fito ne daga jihar Ekiti, Ana tunanin ya dauki cutar ne wajen tuka wani Bako da ya mutu a Najeriya.

Kwamishinar ta ce Direban ya tuka wannan Mutumin kasar waje da wata Baiwar Allah, sai dai Direban ne kadai ya yi rashin sa’ar daukar wannan cuta da ke zagaya Duniya.

Bakon ya kwanta rashin lafiya ne a Ranar Lahadi, inda aka yi maza aka ruga da shi zuwa wani asibiti, kafin ayi iya yi masa wani abu ne dai rashin lafiyar ta kai shi barzahu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel