Gwamnatin Ekiti ta ce an samu Mutumin farko da ya kamu da COVID-19

Gwamnatin Ekiti ta ce an samu Mutumin farko da ya kamu da COVID-19

Labari ya zo mana cewa an samu mutumin farko da ya kamu da cutar coronavirus a Jihar Ekiti da ke Kudancin Najeriya a Ranar Larabar nan, 18 ga Watan Maris, 2020.

Kwamishinar lafiya ta Ekiti, Dr. Mojisola Yaya-Kolade, ta nuna cewa wani Direban mota da kwanaki ya tuka wani Mutumin Amurka ya kamu da cutar a halin yanzu.

Kawo yanzu dai ainihin wannan Bawan Allah da ya zo daga Amurka ya rasu. Ana zargin cewa wanda ya tuka shi daga Garin Ibadan zuwa Ekiti ya dauki cutar a wurinsa.

Gwamnatin Ekiti ta tabbatar da wannan labari mara dadi ne a daren Ranar Laraba. Kwamitin da aka kafa domin yaki da cutar #COVID-19 a jihar ya bayyana haka a jiya.

Mai girma gwamna Dr. John Kayode Fayemi, shi ne shugaban wannan kwamiti da aka kafa. Gwamnan ya ce gwaji ya nuna Direban da ya tuka Ba-Amurken ya kamu.

A cewar Kwamishinar lafiyar, wannan Direban da ya kamu da cutar ya fito ne daga jihar Ekiti, Ana tunanin ya dauki cutar ne wajen tuka wani Bako da ya mutu a Najeriya.

Ga cikakken jawabin da gwamnatin Ekiti ta fitar:

KU KARANTA: COVID-19 ta kashe wani Matashin Kocin wasan kwallon kafa a Sifen

Kwamishinar ta ce Direban ya tuka wannan Mutumin kasar waje da wata Baiwar Allah, sai dai Direban ne kadai ya yi rashin sa’ar daukar wannan cuta da ke zagaya Duniya.

Bakon ya kwanta rashin lafiya ne a Ranar Lahadi, inda aka yi maza aka ruga da shi zuwa wani asibiti, kafin ayi iya yi masa wani abu ne dai rashin lafiyar ta kai shi barzahu.

Dr. Yaya-Kolade ta ce ba a iya kammala gwajin cutar a kan wannan Mutumi da ya zo daga ketare ba, amma babu shakka gwajin da aka yi ya nuna Direban motar ya na da cutar.

Ita kuma wanda ta ke tare da su, ba ta kamu da cutar ba. A dalilin haka aka killace wannan Direba mai shekaru 38. Yanzu haka ana daukar matakin hana yaduwar cutar a Jihar.

Gwamnatin jihar ta yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu, an kuma bada akwatin lambar waya da za a kira domin matsalar: 09062970434, 09062970435, 09062970436.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel