Ganduje ya kalubalanci hukuncin kotu a kan binciken Sanusi II

Ganduje ya kalubalanci hukuncin kotu a kan binciken Sanusi II

- Gwamna da kwamishinan shari'ar jihar Kano a jiya sun kalubalanci hukuncin babbar kotun tarayya da ke zama a jihar Kano

- Kotun ta umarcesu da su daina bincikar tubabben sarki Muhammadu Sanusi II a kan zargin badakalar filayen da ake masa

- Lauyan jihar, Khalifa A. Hashim mai wakiltar Ganduje da antoni janar din jihar, ya shigar da kara mai kalubalantar wannan hukuncin

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da antoni janar din jihar Kano kuma kwamishinan shari'a, Ibrahim Mukhtar, a jiya sun kalubalanci hukuncin babbar kotun tarayya da ke zama a jihar Kano da ta umarcesu da su daina bincikar tubabben sarki Muhammadu Sanusi II a kan zargin badakalar filayen da ake masa.

Lauyan jihar, Khalifa A. Hashim mai wakiltar Ganduje da antoni janar din jihar, ya shigar da kara mai kalubalantar wannan hukuncin na ranar 17 ga watan Maris 2020 wanda kotun ta yanke, kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito.

A ranar 6 ga watan Maris din 2020 ne tsohon basaraken ya tunkari kotun da bukatar ta dakatar da shugaban hukumar sauraron korafi da yaki da rashawa ta jihar Kano din, Muhyi Rimingado, Antoni janar din jihar Kano da kuma gwamnan jihar da su dakata da bincikarsa har sai kotun ta kammala da shari'ar farko. Lamarin kuwa da kotun ta aminta dashi a ranar 18 ga watan Maris din 2020.

Ganduje ya kalubalanci hukuncin kotu a kan binciken Sanusi II

Ganduje ya kalubalanci hukuncin kotu a kan binciken Sanusi II
Source: Twitter

DUBA WANNAN: A raba ni da matata kafin in halaka ta - Magidanci ya sanar da kotu

A lokacin da aka kira shari'ar a jiya, lauyan tubabben sarkin, Nasir Dangiri (SAN) ya sanar da kotun a kan bukatar da Ganduje da Mukhtar suka shigar na kalubalantar hukuncin kotun.

Amma kuma Dangiri ya bukaci karin lokaci don martani ga bukatar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ta Ibrahim Mukhtar, kwamishinan shari'ar jihar Kano.

Alkalin, Mai shari'a Lewis Allagoa, ya dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 23 ga watan Maris din 2020 da kuma sauraron kalubalen da hukuncin kotun ke fuskanta.

Hashim dai shine lauya mai kare Antoni janar da Gwamnan jihar Kano, sai kuma Usman fari wanda ke jagorantar lauyoyin hukumar sauraron korafi da yaki da rashawa ta jihar Kano tare da shugabanta, Muhyi Rimingado.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel