Mutane 475 sun mutu a Italiya a rana guda sakamakon cutar coronavirus

Mutane 475 sun mutu a Italiya a rana guda sakamakon cutar coronavirus

- Mahukunta a kasar Italiya sun bayyana cewa an sake rasa rayuka 475 sakamakon annobar cutar Coronavirus cikin sa’o’i 24 da suka gabata

- A yanzu jimlar wadanda suka mutu sanadiyar cutar Coronavirus ya kama mutum 2,978 a kasar

- Mutanen da suka kamu da annobar a kasar sun karu daga 31,506 zuwa 34,713

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an sake rasa rayuka 475 sakamakon annobar cutar Coronavirus cikin sa’o’i 24 da suka gabata a kasar Italiya. Mahukunta a kasar ne suka sanar da hakan.

A yanzu jimlar wadanda suka mutu sanadiyar cutar Coronavirus ya kama mutum 2,978 a kasar, Hakan na nufin an samu karuwar kaso 19 cikin 100.

Mutane 475 sun mutu a Italiya a rana guda sakamakon cutar coronavirus

Mutane 475 sun mutu a Italiya a rana guda sakamakon cutar coronavirus
Source: Twitter

Mutanen da suka kamu da annobar a kasar wadda ta fi addabar nahiyar Turai sun karu daga 31,506 zuwa 34,713.

KU KARANTA KUMA: Na yafewa wadanda su ka nemi su tunbukeni daga kujera - Oshiomhole

A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamnatin jahar Legas ta sanar da dakatar da gudanar da sallolin Juma’a da taron bauta na Kiristoci a wani mataki na kokarin yaki da yaduwar mugunyar annobar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito kwamishinan harkokin cikin gida na gwamnatin, Anofiu Elegushi ne ya bayyana haka a ranar Laraba inda yace gwamnatin ta hana duk taro da ya haura mutane 50 a duk fadin jahar.

A cewar kwamishinan, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan ganawa da shuwagabannin addinan biyu, ya kara da cewa akwia bukatar jama’a su rage cudanya da juna har sai barazanar annobar ta ragu.

A nasa jawabin babban limamin jahar Legas, Oluwatoyin Abou-Nollah ya bayyana matakin da gwamnatin ta dauka a matsayin abin a yaba, sa’annan ya yi kira ga Musulmai su bi umarnin gwamnati.

Shi ma shugaban kungiyar kiristoci reshen jahar Legas, Alexander Bamgbola yace kungiyarsu ta amince da wannan umarnin gwamnatin, saboda a cewarsa a yanzu ana maganan yadda za’a rayu ne ba maganan addini ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel