Coronavirus: An fasa yin shagalin bikin maulidi a jihar Sokoto
Khalifa Shehu Ahmad Tijjani Inyass ya bada sanarwar cewa an dage taron maulidi Shehu Ibrahim Inyass wanda kungiyar Majm'ul Ahbabu Shehu Ibrahim za ta shirya a garin Sokoto.
Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun Faila Maulana Sheikh Mahi Cisse a cikin wani dan gajeren sakon murya.
A cikin jawabin Sheikh Mahi Cisse, ya bayyana cewa Khalifa Shehu Tijjani Inyass ya bada izinin dage taron ne saboda barkewar cutar coronavirus wacce ta addabi al'ummar duniya baki daya.
Ya kara da kira ga kungiyar a kan ta gaggauta dakatar da dukkan shirye-shiryen maulidin nata.
Idan zamu tuna, Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi a taron da ya yi da manema labarai, ya bada sanarwar dage taron maulidin guda biyu wanda za a yi a garuruwan Abuja da Sokoto.
A wani rahoto na daban, Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya yi ma yan Najeriya bayani game da bullar annobar cutar Coronavirus, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Batan N36.8m a hukumar JAMB: An gano 'macizan' da suka wawure kudin
Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar ta yanke wannan shawara ne bayan wata doguwar muhawara a zauren majalisar a ranar Laraba, inda ta nemi gwamnatin Najeriya ta dauki kwararn matakai domin kare yaduwar cutar a Najeriya.
“Majalisa ta yi kira ga shugaban kasa ya fito ya yi ma yan Najeriya bayani game da wannan matsalar, manyan kasashen duniya sun yi haka, idan ya fito yayi jawabi ga yan Najeriya, sai an fi daukan maganan da muhimmanci." cewar majalisar.
Majalisar ta kara da cewa, “Ba wai mun ce babu abinda take yi bane, amma akwai bukatar gwamnati ta dauki kwararan matakai kamar su hana tafiye tafiye, hana wasu kasashe shigowa kasa, rufe iyakokin kasar, rage taruwar jama’a, tsaurara binciken masu shigowa kasa da kuma killacesu tsawon makonni biyu."
Sanata Danjuma Goje na jahar Gombe ne ya gabatar da wannan kuduri a gaban majalisar, inda yace akwai bukatar gwamnatin tarayya, gwamnatin jahohi da gwamnatocin kananan hukumomi su sanya idanu kamar yadda hukumomin kiwon lafiya suka tanada.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng