Yajin aiki: Mun cimma yarjejeniya kwakkwara da gwamnatin Najeriya - ASUU

Yajin aiki: Mun cimma yarjejeniya kwakkwara da gwamnatin Najeriya - ASUU

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta ce ta cimma matsaya kwakwara da gwamnatin tarayya a kan yajin aikin jan kunne da kungiyar ta tafi a kwanan nan.

Biodun Ogunyemi, Shugaban ASUU ya bayyana hakan a Abuja yayinda ya ke zantawa da manema labarai a karshen ganawar sirri da suka yi da ma’aikatar diban aiki.

An fara ganawar da misalin karfe 3:00 na rana sannan aka kare da karfe 11:00 na ranar Talata.

Ku tuna cewa ASUU ta fara yajin aikin jan kunne a ranar 9 ga watan Maris, 2020 bayan rashin samun matsaya tare da gwamnatin tarayya kan lamaran da suka shafi wasu alawus na makarantun jami’a.

Yajin aiki: Mun cimma yarjejeniya kwakkwara da gwamnatin Najeriya - ASUU
Yajin aiki: Mun cimma yarjejeniya kwakkwara da gwamnatin Najeriya - ASUU
Asali: Facebook

Sauran lamuran da aka ziyarta sune na tsarin biyan kudi bai daya wato IPPIS da sauran lamura da suka shafi kudaden jami’a.

Ogunyemi ya bayyana cewa babu wata sanarwa da za a yi har sai bayan an gabatar da sabbin bukatun gwamnati ga mambobin kungiyar.

A cewar Ogunyemi: “mun yi wasu tattaunawa masu alfanu, mun samu ci gaba a inda muke a baya, muna da abunda za mu kira da muhimman bukatu kuma muna da abun mayarwa da mambobinmu.

“Amma mu kan fadi cewa, mu da muke nan ba za mu iya bayar da sanarwar karshe kan kowani bukata ba sannan mun ba gwamnati tabbatacin cewa za su sanarwa da jiga-jiganmu gaskiya sannan mu dawo wa gwamnati da bayani.

“Muna son ba dukkanin yan Najeriya tabbacin cewa mun damu da son komawa bakin aikinmu kamar kowani mutum, saboda mun san cewa a nan ne muke samun farin ciki, bama farin ciki a wajen ajujuwa, dakunan gwaje-gwajenmu da dakunan karatunmu.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Karo na farko an samu wani da ake zargin yana dauke da coronavirus a jahar Katsina

Ya ce sun dauki wannan mataki da suke kai ne domin amfanin kasa.

Da ya ke magana, Sanata Chris Ngige, ministan kwadago da daukar ma’aikata, ya ce dukkanin bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai amfani kan lamura musamman kan lamarin IPPIS.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel