Yanzu Yanzu: Karo na farko an samu wani da ake zargin yana dauke da coronavirus a jahar Katsina

Yanzu Yanzu: Karo na farko an samu wani da ake zargin yana dauke da coronavirus a jahar Katsina

Ma’aikatar lafiya ta jahar Katsina ta samu wani mutum na farko da ake zargin yana dauke da cutar coronavirus, sakataren din-din-din na ma’aikatar, Dr Kabir Mustapha ya bayyana.

Da yake jawabi ga manema labarai a safiyar yau Laraba, 18 ga watan Maris, Mustapha ya ce mara lafiyar, wanda a yanzu ya killace kansa, ya dawo ne daga kasar Malaysia dauke da alamun cutar da ke bukatar bincike.

“Tuni aka dibi jininsa sannan aka tura domin gwaji kuma ana sanya ran samun sakamako a gobe. Za a fara neman wadanda suka yi hulda dashi ba tare da bata lokaci bad a zaran sakamakon ya fito,” in ji shi.

Yanzu Yanzu: Karo na farko an samu wani da ake zargin yana dauke da coronavirus a jahar Katsina
Yanzu Yanzu: Karo na farko an samu wani da ake zargin yana dauke da coronavirus a jahar Katsina
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa ma’aikatar na daukar dukkanin matakai da kuma aiki kai-da-fata tare da cibiyar kare cututtuka ta kasa (NCDC) kan lamarin.

Sakataren ya shawarci mutanen Dutsinma da su yi taka-tsan-tsan da zirga-zirga da kuma tarurruka.

Ya kara da cewa mutane su nemi kulawar likitoci kai tsaye domin an tanadi duk wasu matakan da suka kamata domin bayar da tallafi.

KU KARANTA KUMA: Likitoci sun tafi yajin aikin sai baba ya gani a Gombe duk da barkewar coronavirus

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa gwamnatin tarayya ta haramtawa matafiya daga kasashe 13 shigowa Najeriya daga yau saboda annobar cutar Coronavirus.

Gwamnatin ta yanke wannan shawara ne domin takaita yaduwar cutar a Najeriya. Kawo yanzu, mutane uku kacal aka tabbatar da sun kamu da cutar a Najeriya.

Kasashen da aka haramtawa shiga Najerya sune Sin, Italiya, Iran, Koriya ta kudu, Andalus (Spain), Japan, Faransa, Jamu, Amurka, Norway, Ingila, Holand, da Swizalan.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana hakan ne da safiyar Laraba, 18 ga Maris, 2020.

Jawabin yace “Gwamnatin tarayya ta hana shigowa kasar ga matafiya daga kasashen Sin, taliya, Iran, Koriya ta kudu, Andalus (Spain), Japan, Faransa, Jamu, Amurka, Norway, Ingila, Holand, da Swizalan.“

“Wadannan sune kasashe masu mutane masu dauke da cutar akalla 1000.“

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel