Gwamna Abiodun ya zare hannunsa daga Kwamishinan da ya zagi Osoba

Gwamna Abiodun ya zare hannunsa daga Kwamishinan da ya zagi Osoba

A Ranar Talata, 17 ga Watan Maris 2020, gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya yi Allah-wadai da Kwamishinan harkokin Matasa da wasanninsa, Mista Oludare Kehinde.

Ana zargin cewa Oludare Kehinde ya fito ya na sukar Aremo Olusegun Osoba, inda ya kira sa Shugaba maras Magaji, wanda hakan bai yi wa Maigidansa gwamna dadi ba.

Olusegun Osoba tsohon gwamna ne a jihar Ogun wanda ya yi mulki har sau biyu. Wannan ya sa gwamna Abiodun ya fito ya bayyana cewa ba shi ya aiki Kwamishinan ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Mai girma gwamna Prince Abiodun ya fitar da jawabi a jiya Ranar Talata ya na sukar kalaman Kwamishinan wasannin da Matasan jihar.

Gwamnan ya ce akwai karambani da kuruciya da neman rigima a kalaman Kwamishinan. Gwamnan ya yi magana ne ta bakin Sakataren yada labaransa, Kunle Somorin.

KU KARANTA: Buhari ya yi wa Gwamna Bello ta'aziyyar rashin Mahaifiyarsa

Gwamna Abiodun ya zare hannunsa daga Kwamishinan da ya zagi Osoba
Gwamna Dapo Abiodun ya yi tir da Kwamishinansa da ya soki Osoba
Asali: UGC

Kunle Somorin ya ce: “Ba sai an fada ba, babu wanda ya aiki Kwamishinan. Prince Dapo Abiodun ya janye kansa da gwamnatinsa daga kalamai marasa dadi na Kwamishinan.”

Gwamnan ya bayyana cewa: “Abin farin cikin shi ne an tattauna wannan magana da Baba, kuma kamar yadda aka saba, ya nuna shi Uba ne kuma shugaban da aka san shi ne.”

Ya ce: “An kira Dr. Oludare Sunday Kehinde domin ya amsa laifin sa. Duk da haka Mai girma gwamna ya na ba Olusegun Osoba hakuri kan kalaman wannan Kwamishina.”

Prince Dapo Abiodun ya ce kalaman Kwamishinan mai shekaru 36 a Duniya ba su nuna yadda gwamnatin jihar Ogun ta ke kallon Mutum mai daraja Aremo Olusegun Osoba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel