Na gaji da yadda wasu mazan ke morar mata ta - Miji ya sanar da kotu

Na gaji da yadda wasu mazan ke morar mata ta - Miji ya sanar da kotu

Wani mutum mai suna Taiwo Oyedeji, dan asalin Ibadan kuma mai siyar da ababen hawa ya sanar da wata kotun gargajiya da ke Ibadan cewa ya gaji da aurensa mai shekaru 17. Ya bukaci kotun da ta tsinke igiyar aurensa da matarsa mai suna Aminat don ba zai iya jure halin cin amanarta ba.

Mai shari’a Ademola Odunade, ya fara sanar da kotun cewa, Taiwo mazaunin yankin Fatusi da ke Ibadan, ya mika bukatar a raba musu aurensu da matarsa don ba zai iya jure rayuwa tare da ita ba. Ya ce ta zama ta kowa don ba shi kadai bane take kwanciya da a matsayin miji.

Ya ce, “A lokacin da na zargi Amina da lalata da mazan waje, na bayyana mata cewa na sani amma sai na shawarceta da ta daina. Hakan kuwa kwarin guiwa kawai ya kara mata. Ta ci gaba da dawowa gida tsakar dare har dai wata rana na kamata dumu-dumu.”

Ya kara da cewa, “Wata rana ta ajiye wayarta sai ga wata lamba tana ta kiranta. Tuni na sauya murya inda mutumin ke sanar dani cewa tun wancan lokacin da suka sha shagalinsu, ya yi tafiya ne. Don haka zai dawo babu dadewa kuma yana so su ci gaba da barnarsu.”

Na gaji da yadda wasu mazan ke morar mata ta - Miji ya sanar da kotu

Na gaji da yadda wasu mazan ke morar mata ta - Miji ya sanar da kotu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Budurwa ta sa an damke mutumin da ya taba mata nono a motar haya

Bayan ya tunkareta ne Amina ta buga masa sanda a wuya.

Aminat dai ta musanta aukuwar duk zargin da mijinta yake yi. Ta ce bayan cin amanarta da yake yi, har kokarin halaka ta yake yi. Ta bayyana yadda Taiwo ya kusan faskara mata kai da gatari kuma ya cika rigima.

A yayin yanke hukunci, Odunade ya tsinke igiyoyin aurensu sannan ya ce babban dansu ya zauna hannun mai kara inda wacce ake karar za ta rike sauran biyun.

Ya kara da bukatar Taiwo da ya dinga biyanta N10,000 a matsayin kudin ciyarwa tare da kuma daukar dawainiyar karatunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel