Shugaban APC Oshiomole ya bayyana darasin da ya dauka daga rikicin APC
Shugaban jam’iyyar APC mai mulki, kwamared Adams Oshiomole ya bayyana cewa ya dauki muhimmin darasi daga rikita rikitan shugabanci da ta dabaibaye jam’iyyar har ma ta kusan yin awon gaba da shi daga kujerarsa.
Jaridar Punch ta ruwaito Oshimole ya bayyana haka ne a ranar Talata, 17 ga watan Maris yayin da yake gabatar da jawabi a sakatariyar jam’iyyar biyo bayan nasarar wucin gadi daya samu a gaban kotun daukaka kara da ta umarci a bashi daman cigaba da shugabancin jam’iyyar har sai ta kammala sauraron shari’ar.
KU KARANTA: Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi
A cewar Oshiomole zai sauya tsarin shugabancinsa ta yadda zai yi daidai da bulkatar yayan jam’iyyar, haka zalika ya yi kira ga shuwagabannin jam’iyyar su kawar da son ransu, su sanya bukatun Najeriya a gaba.
Don haka ya nemi taron farko na shuwagabannin jam’iyyar ta mayar da hankali wajen tattauna matsalar annobar Coronavirus, Oshiomole ya bayyana haka yayin da yake rike da hannun abokin hamayyarsa, Victor Giadom.
Shugaban APC ya ce a yanzu haka kasashen duniya sun garkame iyakokin kasashensu tare da hana baki shigowa don gudun yaduwar cutar, amma har yanzu Najeriya bata bi sawunsu ba, sa’annan ya kara da cewa rikicin da suka fuskanta ba wani sabon abu bane a siyasa.
“Siyasar cikin gidan jam’iyya ya tattara ne bukata, don haka ba ni bane shugaban jam’iyyar da yafi iya tafiyar da jam’iyya a duniya ba, kuma bane ni ne ba, za’a iya samun matsala da salon mulkina, amma ba zaka tuhumi manufata ba.
“Shuwagabannin jam’iyyar nan kansu hade take, babu wanda ke zaune a wurin nan dake da manufar lalata jam’iyyar nan, ina da tsarin salon mulkina, amma zan gyara don duba tsarin wasu.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng