Shawarwari 6 ga mutanen da suke tunanin sun kamu da cutar coronavirus

Shawarwari 6 ga mutanen da suke tunanin sun kamu da cutar coronavirus

Kamar yadda ake ciki a yanzu cutar Coronavirus na ci gaba da yaduwa a fadin duniya, inda a yanzu haka aka samu mutum na uku da ke dauke da cutar a jahar Lagas.

Hakan na ci gaba da wanzar da tsoro a zukatan al’umma, yayinda ake daukar matakan hana yaduwar cutar.

Cutar dai kan fara ne da masassara, sai kuma tari, daga nan kuma sai mutum ya fara fuskantar wahala wajen shakar numfashi.

Don haka muka zakulo maku wasu shawarwari da ya kamata mutumin da ke tunanin ya kamu da cutar zai bi.

Shawarwari 6 ga mutanen da suke tunanin sun kamu da cutar coronavirus
Shawarwari 6 ga mutanen da suke tunanin sun kamu da cutar coronavirus
Asali: Facebook

Ga shawarwarin kamar haka:

1. Ya guji zuwa wurin likita da ke tiyata da kantin siyar da magunguna da asibiti

2. Ya nemi shawara ta hanyar kiran ma’aikatan lafiya ko cibiyoyin lafiya da ke yankin

3. Ana iya bashi shawarar killace kansa

4. Ana iya tura bayansa ga tawagogin lafiya na yankinsa

5. Ana iya yi masa gwajin cutar coronavirus

6. Ma’aikatan Lafiya ko likita na iya bayar da shawara kan matakin gaba da zai dauka idan akwai bukatar hakan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotun koli ta jingine bukatar APC na sake duba hukuncinta a kan zaben Zamfara

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da dage bikin wasanni na kasa (NSF) da aka yi wa lakabi da Edo 2020 a matsayin wani mataki na kare yaduwar cutar Coronavirus a kasar.

Najeriya ta tabbtar da samun bullar cutar ta COVID-19 karo na uku a ranar Talata 17 ga watan Maris na 2020.

Ministan Wasanni na Najeriya Sunday Dare ya sanar da cewa za a dage wasanni na kasar da aka shirya yi a Birnin Benin na jihar Edo.

'Yan wasa a dukkan jihohin kasar sun dade suna shirin zuwa Birnin Benin domin hallartar wannan wasannin kafin sanarwar ta fito a ranar Talata 17 ga watan Maris.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel