Kungiyar SSANU ta yi da-na-sani, ta bi ASUU kan kin amincewa da IPPIS

Kungiyar SSANU ta yi da-na-sani, ta bi ASUU kan kin amincewa da IPPIS

Mun samu labari cewa kungiyar manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya ta SSANU ta janye goyon bayanta ga tsarin biyan albashin IPPIS da aka shigar da Ma’aikatan jami’a.

SSANU wanda a baya ta goyi bayan wannan shiri na IPPIS ce gwamnatin tarayya ta ci amanarta, bayan ta ga ba yadda ta saba gani ba a albashin watan Fubrairun da ya gabata.

A wani jawabi da kungiyar ta fitar a Ranar Litinin ta bakin Mai magana da yawunta, Mista Abdulsobur Salaam, ta ce gwamnati ta yi watsi da yarjejeniyar da aka yi da ita.

Abdulsobur Salaam ya ce idan ba a manta ba SSANU ta yi na’am da tsarin IPPIS ne bayan ta fahimci cewa Akanta Janar zai yi la’akari da tsarin gudanar da Jami’o’in kasar.

A cewar SSANU sun nuna dar-dar din su game da batun biyan alawus da daukar ma’aikata, da karin albashi, da kuma cire kudin hraji, wanda aka yi ta da wajewa da gwamnati.

KU KARANTA: Gwamnati ta sa labule da Shugabannin ASUU kan yajin aiki

Kungiyar SSANU ta yi da-na-sani, ta bi ASUU kan kin amincewa da IPPIS
Bayan wata guda Kungiyar SSANU ta bukaci a maida su cikin GIFMIS
Asali: UGC

Sai dai kuma yanzu kungiyar ta SSANU ta bayyana cewa ta yi mamaki kwarai da ta ga banbanci daga maganar da aka yi da gwamnatin tarayya a albashin watan Fubrairu.

Bayan wannan cin amana, SSANU ta bayyana cewa ‘Ya ‘yanta sun gamu da matsaloli bayan sun shiga wannan tsarin albashi na IPPIS, wanda hakan ya jefa su cikin kunci.

“Wannan ya nuna mana duk da kyautata zaton da mu kayi, wannan gwamnatin ba abin yarda ba ce har abada, ba mu ga laifin Malamai na ASUU da su ka ki shiga IPPIS ba.”

Salam ya ce SSANU ba za su yarda da wannan tsari ba don haka su ka bukaci gwamnati ta daina amfani da IPPIS wajen biyansu albashi, ta bukaci a komawa tsarin GIFMIS.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel