Coronavirus: Za a rufe masallatai da wuraren wanka a kasar Moroko

Coronavirus: Za a rufe masallatai da wuraren wanka a kasar Moroko

Rahotanni sun kawo cewa ana shirin rufe wuraren wanka na jama’a wanda aka fi sani da Hammams domin rage yaduwar cutar Coronavirus a kasar Moroko.

Ministan cikin gida na kasar ne ya fitar da sanarwa a kan wannan mataki da gwamnatin kasar za ta dauka.

Har ila yau ministan ya bayyana cewa za a kulle wuraren shan shayi da gahawa, wuraren cin abinci, sinima da kuma masallatai duk a mataki na hana yaduwar mummunan cutar da ke ci gaba da yaduwa a duniya.

Coronavirus: Za a rufe masallatai da wuraren wanka a kasar Moroko
Coronavirus: Za a rufe masallatai da wuraren wanka a kasar Moroko
Asali: UGC

Ministan ya ce kasuwanni da shaguna da kuma wuraren da ake sayar da abubuwan bukata na yau da kullum ba sa cikin wuraren da za a rufe.

Ya zuwa yanzu dai akwai mutum 29 da suka kamu da cutar a kasar.

KU KARANTA KUMA: Cutar Coronavirus ba ta shigo Yobe ba – Gwamnatin jahar

A wani labarin kuma, mun ji cewa Karamin ministan harkokin kiwon lafiya, Adeleke Mamora ya bayyana cewa an samu wani likita dan Najeriya da ya rasa ransa a sakamakon annobar cutar Coronavirus a kasar Canada.

Daily Nigerian ta ruwaito Minista Mamora ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake bayar da jawabi a kan cutar Coronavirus ga manema labaru inda yace sunan wannan likita dan Najeriya Olumide Okunuga.

“Ya kamata kowa ya zama mai lura da ankara, na ji jama’a na cewa wai bakar fata na da kariya daga cutar Coronavirus, wai ba za ta iya cutar damu ba, don haka nake shaida mana cewa bakar fata kuma dan Najeriya ya mutu a sanadiyyar cutar.

“Mun samu labarin wani likita dan Najeriya dake zama a kasar Italiya wanda ya mutu a sakamakon cutar, don haka akwai bukatar mu yi taka tsantsan game da sauraron batutuwan da basu tabbata ba.” Inji shi.

Rahotanni sun bayyana cewa Dakta Okunugu dan shekara 63 ya kamu da cutar ne yayin wata ziyara daya kai kasar Canada.

Hakazalika a bangare guda mun ji cewa a ranar Litinin, kasar Ghana ta kulle dukkan makarantu da jami'o'inta da duk wani taro domin takaita yaduwar cutar Coronavirus da ta addabi duniya wannan shekaran.

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya sanar da hakan ne ga alummar kasar cewa za a kulle makarantun har ila ma shaa Allahu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel