Oshiomhole: Buhari ya shiga ganawar sirri da gwamnonin APC 16
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga wata ganawar sirri da gwamnonin jam'iyyar APC 16
- An shiga taron ne gabanin taron majalisar zartarwa da ake saka ran zai yanke matsaya a kan shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole
- Gwamnonin da suke cikin taron sun hada da na jihar Borno, Lagos, Ogun, Edo, Kebbi, Jigawa, Kwara, Nasarawa, Niger, Plateu, Ondo, Kano, Osun, Katsina, Imo da Gombe
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga wata ganawar sirri da gwamnonin jam'iyyar APC 16 a fadarsa gabanin taron majalisar zartarwa da ake saka ran zai yanke matsaya a kan shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, da kotu ta dakatar a amakon jiya.
Gwamnonin da suke cikin taron sun hada da na jihar Borno, Lagos, Ogun, Edo, Kebbi, Jigawa, Kwara, Nasarawa, Niger, Plateu, Ondo, Kano, Osun, Katsina, Imo da Gombe.
Daga cikin gwamonin jam'iyyar APC 20, hudu ne kawai bau halarci taron ba. Sun hada da gwamnan jihar Kaduna, Yobe, Kogi da Ekiti.
Batun yunkurin tsige Oshiomhole daga kujerarsa ya gwara kan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC da suka hada da gwamnoni, mambobin majalisa, shugabannin jam'iyya na jihohi, mambobin kwamitin zartarwa (NWC) da sauransu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng