Buhari ya bawa daliban sakandire uku tallafin karatu har matakin digiri na uku

Buhari ya bawa daliban sakandire uku tallafin karatu har matakin digiri na uku

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da tallafin karatu har zuwa matakin digiri na uku ga wasu daliban makarantun sakandire guda uku bayan sun lashe kyautar gasar kyautar shugaban kasa ta matasan daliban kimiyya na Najeriya.

Tallafin zai bawa dabilaban damar zaben kowanne bangare na karatun ilimin kimiyya a duk jami'ar da suke so a fadin Najeriya har su kammala digirinsu na uku.

A jawabin da ya gabatar a wurin taron bayar da kyauta ga daliban, shugaba Buhari ya yaba wa masu shirya gasar tare da daliban da suka samu nasara a cikin dalibai 774 da suka shiga gasar matasan daliban kimiyya na shekarar 2020.

Daliban da suka samu damar lashe kyautar kuma suka samu tallafin sune; Masters Akintade Abdullahi Akanbi daga makarantar sakandiren Osogbo a jihar Osun, wanda shine ya zo na farko gasar; sai wanda ya zo na biyu, Nelson Kansiyochukwu daga makarantar sakandire ta 'British Spring College' a jihar Anambra, da Aimofumhe Eshiobomhe Sigmus daga makarantar hazikan yara da ke Gwagwalada, Abuja, wacce ta zo na uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel