Ganduje da kansa ya kirani ko zan karbi Sunusi a Nassarawa – Gwamna Sule

Ganduje da kansa ya kirani ko zan karbi Sunusi a Nassarawa – Gwamna Sule

Gwamnan jahar Nassarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kansa ne ya kira shi a waya, kuma ya shaida masa niyyarsa na tsige Sarkin Kano Muhammadu Sunusi.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a jahar Legas, inda yace ya zama wajibi ya yi wannan karin haske, saboda Ganduje da kansa ya nemi izininsa domin ya kori Sunusi zuwa jahar.

KU KARANTA: Jami’in Dansanda ya dirka ma kansa harsashi bayan ya bindige matarsa har lahira

Ganduje da kansa ya kirani ko zan karbi Sunusi a Nassarawa – Gwamna Sule

Ganduje da kansa ya kirani ko zan karbi Sunusi a Nassarawa – Gwamna Sule
Source: Twitter

“Jim kadan bayan an tsige shi, sai gwamnan Kano ya kira ni ya fada min cewa yanzu nan suka tsige Sarkin Kano, kuma suna tunanin mayar da shi jahar Nassarawa ya tambaye ni ko zan amshe shi, ni kuma na fada masa a shirye nake na karbe shi.

“Labarin tsige Sarkin na ta yawo a kafafen sadarwar zamani, amma ban duba ba saboda ina ta aiki, amma da gwamnan ya kira ni, sai hadimina ya kawo min wayar yayin da nake cikin ganawa da wasu mutane.

“Saboda girmansa da nake gani, kuma babban gwamna duba da yana wa’adi na biyu ne, don haka sai na fita daga ganawar na amsa wayarsa, duk duniya kowa ya san suna da matsala, amma ban taba tunanin za ta kai ga haka ba.” Inji shi.

A lokacin da nake babban manajan kamfanin Dangote, shi kuma yana shugaban bankin First Bank, a lokacin da na zama mataimakin manajan kungiyar Dangote gaba daya, shi kuma ya zama gwamnan CBN, zuwa lokacin da na zama shugaban kungiyar Dangote gaba daya kuma, ya zama Sarki, don haka mun dade muna mu’amala.

Da yake jawabi a kan abin da yasa jahar Nassarawa ta zamo garin da ake yawon ajiye Sarakunan da aka fatattaka, sai yace ba komai bane yasa haka illa kasancewar jahar a tsakanin iyakar jahohin kudu da jahohin Arewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel