Za a hana masu laifi takarar Gwamna da Shugaban kasa a Najeriya

Za a hana masu laifi takarar Gwamna da Shugaban kasa a Najeriya

- Majalisa na shirin hana masu laifi takarar Gwamna da Shugaban kasa a Najeriya

- Dalilin wannan doka shine domin a hana irin wadannan mutane yin takara a zabukan kasar na gaba

- Shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan rundunar sojoji Abdulrazaq Namdas ne ya gabatar da bukatar a gaban majalisar wakilai

Wata doka da ke neman a haramta wa wadanda ke da tarihin aikata laifi imma a Najeriya ko waje yin takarar mukamin shugabanci na siyasa na kan hanya a majalisar wakilai.

Dalilin wannan doka shine domin a hana irin wadannan mutane yin takara a zabukan kasar na gaba.

Za a hana masu laifi takarar Gwamna da Shugaban kasa a Najeriya

Za a hana masu laifi takarar Gwamna da Shugaban kasa a Najeriya
Source: Facebook

Abdulrazaq Namdas (APC Adamawa) ne ya gabatar da dokar mai taken “National Convict and Criminal Records (Registry) Bill, 2020”.

Namdas ya kuma kasance Shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan rundunar sojoji.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, dokar ya nemi a durkushe kudirin yan siyasa da ke da laifuffuka.

Dokar na kuma so wurin rijistan ta yi aiki tare da rundunar yan sanda, hukumar gidan yari da sauran hukumomin tsaro wajen gano masu laifin.

KU KARANTA KUMA: Muhammadu Sanusi: Sheikh Gumi ya caccaki tsohon sarkin kan hawa motar Rolls Royce

Dokar na kuma neman a ba rijistan ikon kamawa da hukunta masu neman aiki da masu takarar siyasa wadanda aka samu da tarihin aikita laifi.

A wani labari na daban, mun ji cewa ‘Dan takarar jam’iyyar APC a zaben kujerar majalisar tarayya na Yankin Babura da Garki a jihar Jigawa ne ya lashe zaben da aka yi a Ranar Asabar dinnan da ta gabata.

Kamar yadda mu ka samu labari daga hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, Muhammad Fagen-Gawo, ya lashe wannan kujera ta tarayya bayan ya samu kuri’u 48, 318.

An gudanar da wannan zabe ne a rumfuna 302 da ke cikin kananan hukumomin Garki da Babura. Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben ofishinta da ke Babura a jiya.

Farfesa Ahmed Kutama wanda ya yi aiki a matsayin Malamin wannan zabe ya sanar da cewa ‘Dan takarar APC Fagen-Gawo shi ne ya yi galaba a kan sauran ‘Yan takarar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel