Sojojin kasa sun lallasa ‘Yan ta’addan Boko Haram a Adamawa da Borno

Sojojin kasa sun lallasa ‘Yan ta’addan Boko Haram a Adamawa da Borno

Mun samu labari cewa Dakarun Sojojin kasan Najeriya na Operation Lafiya Dole sun lallasa ‘Yan ta’addan Boko Haram da su ka fitini Yammacin Afrika da bagarorin Najeriya.

Babban Jami’in Sojan da ke lura da sha’anin yada labarai a Najeriya, Kanal Aminu Ilyasu, ya fitar da wani jawabi a Ranar Lahadi, ya na bayyana irin nasarar da Soji su ka samu.

Kanal Aminu Ilyasu ya shaidawa Jama’a cewa Rundunar Sojojin kasar sun aukawa ‘Yan ta’addan Boko Haram a Garuruwan Damboa da Garkida da ke Borno da kuma Adamawa.

Aminu Ilyasu ya ke cewa an yi wa ‘Yan Boko Haram lahani da wannan hari da aka kai masu a ‘yan kwanakin nan. Ana sa ran hakan zai taimaka wajen kassara ‘Yan ta’addan.

Da ya ke bayani, Jami’in sojan ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘Yan ta’addan na Boko Haram sun mika wuya ga Dakarun Najeriya. Jaridar Daily Trust ta bayyana mana wannan.

KU KARANTA: An zargi wasu tsofaffin Gwamnoni 3 da hannu wajen kirkiro Boko Haram

Sojojin kasa sun lallasa ‘Yan ta’addan Boko Haram a Adamawa da Borno

Operation Lafiya Dole sun ci karfin 'Yan Boko Haram a Adamawa da Borno
Source: Twitter

Ilyasu ya bada sunayen wadanda su ka mika kansu da kansu ga Dakarun Bataliya ta 202 da: Musa Mohammed da Maina Liman wadanda su ke da shekara 21 da kuma 35 a Duniya.

Wadannan ‘Yan ta’adda sun mika wuya ne a Ranar 5 ga Watan Maris. ‘Yan ta’addan sun kuma bayyana cewa su na yi wa wani babban Sojan Boko Haram mai suna Nakib aiki.

Nakib wanda ya kai matsayin Kyaftin a cikin Rundunar ‘Yan ta’addan ya na zaune ne a wani Kauye mai suna Bula Umar kamar yadda Liman da Mohammed su ka bayyana.

Bayan sun shiga hannun Jami’an tsaro, Mohammed da Liman sun bayyana cewa Sojojin Najeriya sun kashe Mayakan Boko Haram da-dama a hare-haren da su ka kai kwanaki.

Rundunar Sojin Najeriya ta shaidawa hukumar dillacin labarai cewa wannan ya nuna akwai Mayakan Boko Haram rututu da ke neman mika wuya domin sun gaji da yakin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel