Irin kokarin da Buhari ya yi don ganin ba a tsige Sanusi II ba - Fadar shugaban kasa

Irin kokarin da Buhari ya yi don ganin ba a tsige Sanusi II ba - Fadar shugaban kasa

Sabanin zargin da wasu ke yi a kan cewa akwai hannun shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a sauke tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, fadar shugaban kasa ta ce shugaba Buhari ya yi yunkurin warware rikicin da ya kunno kai tsakanin masarauta da gwamnatin Kano a shekaru biyu da suka gabata.

Wata majiya a fadar shugaban kasa da ta nemi a boye sunanta, ta sanar da manema labarai cewa kokarin fadar shugaban kasa na waware rikicin da ke tsakanin Ganduje da Sanusi bai samu ganin hasken rana ba saboda kowanne bangare ya kafe a kan ra'ayinsa.

A cewar majiyar, tun a shekarar 2017 sarki Sanusi ya garzaya wurin shugaba Buhari domin sanar da shi niyyar gwamnatin jihar Kano na raba shi da kujerar sarkin Kano.

Sanusi ya nemi shawarar shugaban kasa, kuma nan take shugaba Buhari ya ce hakan ba daidai bane tare da bayar da umarni a jingine maganar sauke shi a gefe.

"Bayan ganawarsu, shugaban kasa ya aika wa Ganduje takarda a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2017, inda a ciki ya bayar da wannan shawara.

"Shugaban kasa ya umarci shugaban ma'aikatansa, Abba Kyari, ya bibiyi batun domin ganin an warware matsalar cikin maslaha," a cewar majiyar.

Majiyar ta bayyana cewa hakan ne yasa aka kafa wani kwamiti na gwamnoni biyar a karkashin jagorancin gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

A cewar majiyar, an samu daidaituwar al'amura sakamakon shiga lamarin da kwamitin gwamnonin ya yi, amma daga bisani sai al'amura suka kara dagulewa a kan batun sake zaben gwamna Ganduje a karo na biyu.

Irin kokarin da Buhari ya yi don ganin ba a tsige Sanusi II ba - Fadar shugaban kasa

Buhari da Sanusi II
Source: Twitter

"Tun a lokacin rigingimun zaben 2019 gwamnan Kano ya so cire Sanusi, amma sai gwamna Fayemi da takwaransa na jihar Jigawa, Abubakar Badaru, da babban sifeton rundunar 'yan sanda suka lallashi gwamnan a kan ya hakura da cire sarkin saboda dalilan tsaro.

"Babban zunubin sarkin a wurin gwamnatin jihar Kano shine yadda ya gaza kawar da kansa daga al'amuran siyasa, musamman siyasar da ta shafi sake zaben gwamnan Kano.

"Bayan wasu dattijan kasa irinsu Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalami Abubakar sun bayar da shawarwari a kan rikicin sarkin da gwamna, sai Abba Kyari ya kafa kwamiti a karkashin Abdulsalami bayan ya nemi izinin shugaban kasa.

"Kwamitin ya zauna tare da shugaba Buhari domin sanar da shi manufofinsa. Yayin ganawarsu, shugaba Buhari ya zayyana musu irin kokarin da ya yi a baya wajen kawo karshen rikicin da ke tsakanin gwamnatin jihar Kano da masarauta tare da sanar da su cewa shi abinma ya ishe shi haka.

"Amma, duk da haka, ya bawa kwamitin tabbacin cewa za su samu goyon baya da hadin kansa a duk lokacin da suke bukata, sannan kuma ya yi fatan alheri tare da fada musu cewa ba zai yi sanya wajen saka dokar ta baci a jihar Kano ba idan al'amura suka rincabe," a cewar majiyar.

DUBA WANNAN: 'Zan iya komawa kan kujerata idan hakan nake so' - Bidiyon Sanusi a kan dalilin kin zuwa kotu

Majiyar ta cigaba da cewa, kwamitin Abdulasali bai samu nasarar kawo karshen rikicinba saboda yanayin sharudan da kowanne bangare ya bayar a kokarin yi musu sulhu.

Duk da hakan, shugaban kasa bai gaza ba a kokarinsa na tabbatar da an samu zaman lafiya a tsakanin shugabannin biyu, a cewar majiyar.

Majiyar ta shugaban kasa ta ce' ko a kwanakin baya bayan nan da Abba Kyari ya wakilci tawagar fadar shugaban kasa zuwa gaisuwar Dan Iyan Kano, Ambasada Sunusi, sai da ya kebe da Sanusi da Ganduje daban-daban domin kokarin yi musu sulhu.

A cewar majiyar, rashin adalci ne a zargi shugaba Buhari da bawa Ganduje umarnin ya sauke Sanusi daga kan kujerar sarkin Kano. Kazalika, ya bayyana cewa fadar shugaban kasa bata da wata matsala da Sanusi, a saboda haka babu hannun Buhari a sauke shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel