Kannywood: Fitacciyar jaruma, Ladi Mutu-ka-raba, ta mutu

Kannywood: Fitacciyar jaruma, Ladi Mutu-ka-raba, ta mutu

Da yammacin jiya, Asabar, ne rahotanni suka bayyana rasuwar fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Ladi Mohammeed, wacce aka fi sani da 'Ladi-mutu-ka-raba'.

A sanarwar da Legit.ng ta samu da yammacin ranar Asabar, an bayyana cewa jarumar ta rasu ne bayan ta sha fama da doguwar jinya.

Jama'a da dama da suka hada da jarumar masana'antar Kannywood sun nuna alhini tare da fara aika ko wallafa sakon yin ta'aziyya mutuwar jarumar.

Fitacciyar jarumar fim, Saratu Gidado, ta wallafa sakon ta'aziyyar mutuwar Ladi mutu-ka-raba a shafinta na dandalin sada zumunta (Instagram)

Kazalika, manyan jarumai irinsu Alihu Nuhu da Sani Musa Danja ba a barsu a baya ba wajen wallafa nasu sakon ta'aziyyar a shafinsu na 'Instagram'.

A shekarar da ta gabata ake ta yawo da hotunan jarumar a shafin dandalin sada zumunta da sunan neman taimako bayan rashin lafiyarta ta yi tsanani.

Amma daga baya marigayiyar ta fito ta karyata batun cewa tana neman taimako tare da bayyana hakan a matsayin sharrin makiya da ke son bata mata suna.

Jarumar ta fito a fina-finan Hausa masu dumbin yawa amma shirin da ya fara haska tauraronta shine fim din 'Mutu ka raba', kamar yadda Ibrahim Sheme ya sanar da sashen Hausa na BBC yayin da suka tuntube shi dangane da mutuwar jarumar.

Source: Legit.ng

Online view pixel