FG za ta rage farashin litar man fetur

FG za ta rage farashin litar man fetur

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta fara tuntubar masu ruwa da tsaki a niyyarta ta rage farashin litar man fetur sakamakon karyewar darajar man fetur a kasuwar duniya.

Karamin ministan harkokin man fetur na kasa, Mista Timipre Sylva, ne ya bayyana hakan ranar Juma'a a Abuja.

Sylva, wanda ya jagoranci wani kwamiti na musamman da ya kafa, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa, Villa.

Ministan ya kafa kwamitin ne domin ya yi duba, nazari tare da bayar da shawarwai a kan tasirin bullar 'Corona Virus' a kan tattalin arzikin Najeriya.

FG za ta rage farashin litar man fetur
Timipre Sylva
Asali: UGC

Sylva, tsohon gwamnan jihar Bayelsa a jam'iyyar PDP, ya bayyana cewa har yanzu ba a tsayar da wata shawara a kan sabon farashin da za a mayar da litar man fetur ba, tare da bayyana cewa an fara tuntuba ne kawai.

DUBA WANNAN: Shekau ya mayar da martani bayan saka kyautar $7m ga duk wanda ya kama shi (Bidiyo)

"Tuntuba muke yi har yanzu, mu na kuma cigaba da bibiyar abubuwan da ke faruwa. Ana saka farashin litar man fetur ne bisa la'akari da farashin danyen man fetur.

"Ku cigaba da hakuri, za mu waiwaye ku," a cewar ministan.

Farashin danyen man fetur ya fara fadu wa a kasuwar duniya tun watan Janairu bayan shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin kudin kasa na shekarar 2020 a watan Disamba, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel