Dalilin da yasa ba zan kalubalanci tube min rawani ba - Bidiyon Sanusi II

Dalilin da yasa ba zan kalubalanci tube min rawani ba - Bidiyon Sanusi II

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da gwamnatin Kano ta tsige daga kan karagarsa ta mulki, ya bayyana yadda zai iya koma wa kan gadon sarauta idan yana son hakan.

Tsohon sarkin ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya bulla a yanar gizo, inda yake cewa gwamnatin Kano ba ta bi ka'aida ba wajen tube masa rawani.

"Dalilin da suka bayar na cire ni shine 'wai' rashin biyayya ga ikon siyasa, eh, haka suka ce [dariya].

"Allah ne ya ara min rana kuma na yi iyakar bakin kokarina a cikin shekaru shidda da na yi a kan mulki. Ba na sha'awar koma wa kan kujerar sarauta.

DUBA WANNAN: Abinda Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fada a kan tsige Sanusi II (sautin murya)

"Maganar gaskiya shine zan iya koma wa kan kujerata idan hakan nake so. Basu bi ka'ida k nuna kwarewae aiki ba wajen cire ni. Ina shigar da kara kotu za ta mayar da ni kan kujerata saboda ba a bani damar kare kaina ba, ba a gurfanar da ni ba, ko kirana basu taba yi don yi min wasu tambayoyi da ya kamata na amsa ba. Rana tsaka kawai suka ce sun cire ni.

"Babu wani abin damuwa, zan cigaba da sabuwar rayuwata," a cewarsa.

A ranar Litinin, 9 ga watan Maris, ne sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya saki jawabi kan dalilin da yasa gwamnatin jiha Kano ta tunbuke Sanusi II daga kan kujerarsa. Ya ce an kwancewa Sanusi Lamido Sanusi rawani ne saboda yana zubar da mutuncin sarauta da kuma nuna halin 'ko oho' a kan sabbin dokokin masarautun jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel