Fasto ya yi wa Sanusi II da iyalansa addu'a a Legas

Fasto ya yi wa Sanusi II da iyalansa addu'a a Legas

- Wani fasto yayi wa tubabben sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ya isa filin sauka da tashin jiragen sama a Legas addu'a

- Sanusi ya isa jihar Legas din ne a jirgin shata mai lamba N5500JF sannan ya kwashe kusan mintoci talatin a filin jirgin

- Babban faston Trinity House da ke Legas, Ituah Ighodalo, yayi addu’a ga Ubangiji a kan ya karesa da iyalansa kafin su fita daga jirgin

Wani fasto yayi wa tubabben sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ya isa filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas a sa’o’in karshe na ranar Juma’a, addu'a.

Sanusi ya isa jihar Legas din ne a jirgin shata mai lamba N5500JF sannan ya kwashe kusan mintoci talatin a filin jirgin , kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Tun bayan saukarsa daga jirgin saman, matansa, ‘ya’yansa da wasu daga cikin ‘yan uwansa suka samu shiga wajen jira a filin jirgin inda aka yi addu’a ta musamman.

Babban faston Trinity House da ke Legas, Ituah Ighodalo, yayi addu’a ga Ubangiji a kan ya karesa da iyalansa kafin su fita daga jjirgin don shiga tawagarsu mai motoci 10.

Fasto ya yi wa Sanusi II da iyalansa addu'a a Legas

Fasto ya yi wa Sanusi II da iyalansa addu'a a Legas
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Daga karshe: Sanusi II ya bayyana wadanda suka bada umarnin tsare shi

A yayin addu’ar, faston ya ce: “Idan wata kofar ta rufe, wata kofar na budewa sannan sharrin da mutane ke fata yana komawa alheri. Don haka muna godiya ga Ubangiji a kan yadda ya kawo tsohon sarkin, dan uwanmu, mahaifinmu, mijinmu kuma kawunmu.”

Ya kara da cewa, “Muna godiya gareka Ubangiji da baka kunyata shi ba kuma muna kara godiya da yadda zaka mayar masa da alkhairi. Muna yi wa Najeriya fata nagari tare da samun sauyi nagari.”

Bayan saukar basaraken daga jrigin saman, ya ki zantawa da manema labarai a kan abinda ya faru dashi. Bayan ya fito daga jirgin saman yayin jiran shiga mota, manema labarai sun bukaci ya bayyana yadda yake ji bayan kwanakin da yayi a tsare.

Amma kuma sai basaraken yayi murmushi tare da cewa “Babu tsokaci” a yayin da aka jagorancesa zuwa mota mai kirar SUV da ke da lamba APP 674 FU.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel