Dalilin da yasa na ziyarci 'Gwarzon duniya' a Awe - El- Rufai

Dalilin da yasa na ziyarci 'Gwarzon duniya' a Awe - El- Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana tubabben sarki a matsayin gwarzon duniya

- Tubabben sarkin ya samu 'yancin shi ne bayan sa'o'i kadan da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin gaggauta sakin shi

- Sarkin Kano na 14 ya samu magaji bayan sa'o'i kadan da tube shi kuma yana kan hanyarshi ta Nasarawa

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana tubabben sarki a matsayin gwarzon duniya wanda ya san kowa kuma akan san shi a duniya.

El-Rufai wanda ya je Awe a ranar Juma'a, ya ce ya je ne don kara ga tubabben sarkin. Ya yi sallar Juma'a a garin wacce Sanusi II ya ja.

"Mai martaba Sanusi gwarzon duniya ne. Nazo mishi kara ne," ya ce.

El-Rufai da Sanusi II sun bar Awe inda suka isa Lafia a ranar Juma'a.

Dalilin da yasa na ziyarci 'Gwarzon duniya' a Awe - El- Rufai

Dalilin da yasa na ziyarci 'Gwarzon duniya' a Awe - El- Rufai
Source: Twitter

KU KARANTA: Sha'awa na damunmu, muna bukatar maza don kwanciya - Matan gidan yari

Tubabben sarkin ya samu 'yancin shi ne bayan sa'o'i kadan da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin gaggauta sakin shi. An kai tubabben Sarkin Awe ne bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya tube mishi rawanin sarautar jihar. An tube mishi rawanin ne sakamakon zargin shi da ake da rashin biyayya ga ofishin gwamna da sauran cibiyoyin gwamnati.

Sarkin Kano na 14 ya samu magaji bayan sa'o'i kadan da tube shi kuma yana kan hanyarshi ta Nasarawa. Aminu Ado Bayero ne ya maye gurbin shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel