Jami’an tsaro sun bindige matashin da yayi kokarin ‘damko’ Buhari a Argungu

Jami’an tsaro sun bindige matashin da yayi kokarin ‘damko’ Buhari a Argungu

Wani matashi da aka yi ta rirrike shi yayin da ya kutsa kai cikin taron baje kolin kayan amfanin noma da kama kifi a garin Argungun inda ya yi kokarin damko shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha wutar alburushi.

Idan za’a tuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci bikin al’adun gargajiya na kamun kifi da noma da aka gudanar a garin Argungu na jahar Kebbi karo na farko bayan kwashe tsawon shekaru 11 ba tare da an yi shi ba.

KU KARANTA: Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari

Jami’an tsaro sun bindige matashin da yayi kokarin ‘damko’ Buhari a Argungu

Jami’an tsaro sun bindige matashin da yayi kokarin ‘damko’ Buhari a Argungu
Source: Facebook

Mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, Mista Femi Adesina ne ya bayyana haka inda yace shugaba Buhari ya bayyana dawowar bikin a matsayin wata manuniya dake nuni ga nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen inganta tsaro a Najeriya.

Daily Trust ta ruwaito an hangi matashin yana ta kokarin kusantar shugaba Buhari a daidai lokacin da ya tsaya tare da manyan baki domin daukan hoto, kwatsam sai ya kutsa kai har gab da Buhari, da kyar jami’an tsaro suka cimimiye shi.

Bayan jami’an tsaro sun dauke shi ne, sai kuma suka dirka masa harsashi a kafa domin su illata shi idan ma yana da wata muguwar manufa a game da shugaban kasar, daga nan kuma jami’an hukumar DSS suka yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da ba’a sani ba.

Ko da majiyar Legit.ng ta tuntubi kaakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu game da lamarin, sai yace: “Masoyin shugaban kasa ne mai rawar kai wanda yayi kokarin kusantar shugaban, amma bai san ya wuce gona da iri ba.” Inji shi.

Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa matashin yana jin haushin shugaban kasa ne, wannan ne dalilin da yasa ya yi kokarin kai masa cafka.

A wani labarin kuma, Buhari ya ce: “Halartarmu yau a bikin baje kolin amfanin noma a garin Argungu tabbaci ne na manufarmu na inganta tsaro tare da fadada hanyoyin samar da abinci a cikin gida, muna sane da cewa an dakatar da wannan biki na shekara shekara tsawon shekaru 11 saboda matsalar tsaro.

“Amma cikin ikon Allah a yau bikin ya dawo, kuma ina fatan ya dawo da alheri, baya ga murnar dawowar wannan biki, muna farin cikin cigaba da aka samu a fannin samar da tsaro a yankin nan, ina kara sanar daku cewa an fara gasar tseren motoci daga Abuja zuwa Argungu a ranar Laraba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel