Darajar Naira ta fadi warwas a kasuwar bayan fage, ana siyar dad ala kan N420

Darajar Naira ta fadi warwas a kasuwar bayan fage, ana siyar dad ala kan N420

Rahotanni sun kawo cewa a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris, farashin chanja naira na tsakanin N405 da N420 kan kowani dala guda a kasuwar bayan fage.

Shugaban kungiyar masu sana’ar chanja kudi na Najeriya, Aminu Gwadabe, ya ce faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya zuwa dala 35 kan kowace gangar mai, ya sa yan chanji da ma yan Najeriya shiga hali na rashin tabbass.

Ya ce wannan hali na rashin tabbass da aka shiga a kasuwa abu ne da bai zama dole ba.

Darajar Naira ta fadi warwas a kasuwar bayan fage, ana siyar dad ala kan N420
Darajar Naira ta fadi warwas a kasuwar bayan fage, ana siyar dad ala kan N420
Asali: UGC

Ya ce: “Da wannan faduwa ta farashin danyen mai a ranar Litinin, mun samu masu zuba jari na waje da dama da suka janye kadarorinsu, musamman don mayar dashi zuwa tsabar kudi.

“Yunkurin ya kasance ne sakamakon sakaci ta bangaren masu chanjin, lokacin da suka so shiga kokwanto, amma babu bukatar hakan saboda babban bankin Najeriya ya ci gaba da tallafawa bangaren chanji.”

Yayinda ya ke bayyana cewa an siyar da dala kan N400, ya ce a hankali lamarin ya sauko domin an saida shi kan N375 kafin rufewar ranar.

A cewarsa, CBN ya tsaya kan N360 sama da shekaru uku da suka gabata.

Ya ce a ganawarsa da CBN a ranar Alhamis, mai kula da lamarin ya gargadi kungiyar kan saba ka’ida.

Shugaban yan chanjin ya bayyana cewa CBN ya so janye lasisin wasu masu chanji a wurare daban-daban amma sai ya ci tarar sama da yan chanji 100 naira miliyan 5 kan laifuffuka daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Cutar yunwa na kashe yan Najeriya fiye da Coronavirus - Sultan

Wani dan chanji da ya zanta da manema labarau ya ce: “Da muka wayi gari a ranar Litinin, farashin chanji na nan a kan kimanin N360, amma kawai saboda faduwar farashin danyen mai, sai mutane suka fara tsoro."

A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta fara biyan N30,000 a matsayin ma fi karancin albashi ga 'yan fansho a jihar biyo bayan sabunta tsohon tsarin biyan 'yan fansho da aka yi a cikin watannan.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da Muyiwa Adekeye, mai bawa gwamna El-Rufa'i shawara a kan sadarwa da kafafen yada labarai, ya fitar ranar Alhamis a Kaduna.

A cewar jawabin, sabon tsarin zai rabauta 'yan fansho 11,511 wadanda zasu fara daukan N30,000 a karshen wata, sabanin tsohon albashinsu wanda bai kai ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel