'Ka zauna da mu har abada' - Mutanen garin Awe sun roki Sanusi II

'Ka zauna da mu har abada' - Mutanen garin Awe sun roki Sanusi II

Mutanen garin Awe a jihar Nasarawa sun bayyana zuwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin babban abun alheri da ya taba samun garinsu, sannan ya kara masa suna da daukaka.

Da yawa daga cikin mazauna garin Awe, hedikwatar karamar hukumar Awe, da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya samu tattauna wa da su sun bayyana farin cikinsu da zama masu masaukin tsohon sarki da aka tubu ranar Litinin.

Dauda Muhammad Awa, mazaunin garin Awe, ya bayyana cewa duk da bai ji dadin cire Sanusi II daga kujerar sarki ba, ya kasance mai alfahari da samun kansa a zaune a gari daya da tsohon sarkin.

"Ba mu ji dadin samun labarin tsige shi ba, amma mun kasance masu sa'a da aka kawo mana shi domin ya zauna a garinmu domin zuwansa alheri ne," a cewarsa.

'Ka zauna da mu har abada' - Mutanen garin Awe sun roki Sanusi II

Gidn Sanusi II a garin Awe
Source: Facebook

Sannan ya cigaba da cewa, "tun da aka kawo shi jama'a ke tururuwar zuwa domin su gana da shi duk da jami'an tsaro suna hana wa. Tunda aka kawo shi sunan garin Awe ya shiga bakin kowa."

Wani mazaunin garin mai suna Dauda Ibrahim ya bayyana cewa an samu karin tsaro a garin Awe saboda an kawo Sanusi II.

DUBA WANNAN: Abinda Sheikh Dahiru Bauchi ya fada a kan tube Sanusi II (sautin murya)

Fatima Kande, wata mazauniyar Awe, cewa ta yi zasu tabbatar da cewa Sanusi II ya ji dadin zaman garin.

"Mutanen garin Awe suna da son zaman lafiya ga karamci, suna karrama bako daga ko ina yake a fadin Najeriya.

"Za mu yi iya bakin kokarinmu wajen ganin tsohon sarkin ya ji dadin zamansa a nan, mu na fatan wataran zai yanke shawarar cewa zai cigaba da zamansa a nan har abada," a cewar Kande.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel