Abu 1 da Sunusi ke yi wanda ke kunyata gwamnatin Ganduje da ta Buhari – rahoton Abdulsalami

Abu 1 da Sunusi ke yi wanda ke kunyata gwamnatin Ganduje da ta Buhari – rahoton Abdulsalami

Binciken kwamitin sulhu tsakanin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi da gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranta ta bayyana cewa furucin Sarkin Kano na kunyata gwamnatin jahar da gwamnatin tarayya.

Kwamitin ta kara da cewa matakin da gwamnatin jahar ta dauka na raba masarautar ya tsoma masarautar Kano cikin matsala, ta yadda ta gagara biyan albasussukan ma’aikatan da ke karkashinta ba.

KU KARANTA: Jami’an tsaro guda 40 ne suke tsaron tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi a Nassarawa

Haka zalika matakan da Sarkin ya dauka na shigar da gwamnatin jahar kara yana kalubalantar kirkirar masarautun Gaya, Rano, Karaye da Bichi ya bata ma gwamnati rai, wanda hakan yasa ta dauke shi a matsayin rashin da’a.

“Maganganun da Sarki yake yawan furtawa suna ja ma gwamnatin jahar Kano bakin jini da ma gwamnatin tarayya, tare da kunyatasu, wanda hakan ya baiwa ma wasu daman kara dagula alakar dake tsakanin bangarorin biyu, har ta kai ga an raba masarautar.

“Gwamnan ya dage a kan cewa lallai ya raba masarautar ne don kawo cigaba a jahar Kano, amma Sarkin na kallon matakin ne a matsayin ladabtarwa a gare shi, don haka kirkirar sabbin masarautun yasa masarautar Kano ta shiga mawuyacin halin biyan albashi.

“Tun daga nan ruwa ta kata tsami tsakani gwamnan da Sarkin, daga nan ta bayyana lokaci kawai ake jira a tsige Sarkin.” Inji rahoton kwamitin.

A bangarensa, Abdulsalami yace tsige Sarkin Kano da Ganduje ya yi ya nuna cewa aikin banza kawai suka yi wajen sulhunta su, tare da bata lokacinsu.

A hannu guda kuma, rahotanni sun tabbatar da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya kai ma amininsa, tsohon sarkin masarautar Kano, Muhammadu Sunusi II ziyara a sabon gidansa da yake zaman hijira a a Awe, jahar Nassarawa.

Majiyoyi daga hukumomin tsaro ne suka tabbatar mata da ziyarar gwamnan, inda suka ce Gwamna El-Rufai ya tashi daga Kaduna ne da safiyar Alhamis, 12 ga watan Maris ya nufi Awe don ganawa da Sarki mai murabus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel