El-Rufai ya kai ma Malam Muhammadu Sunusi II ziyara a Awe

El-Rufai ya kai ma Malam Muhammadu Sunusi II ziyara a Awe

Rahotanni sun tabbatar da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya kai ma amininsa, tsohon sarkin masarautar Kano, Muhammadu Sunusi II ziyara a sabon gidansa da yake zaman hijira a a Awe, jahar Nassarawa.

Daily Trust ta ruwaito wasu majiyoyi daga hukumomin tsaro ne suka tabbatar mata da ziyarar gwamnan, inda suka ce Gwamna El-Rufai ya tashi daga Kaduna ne da safiyar Alhamis, 12 ga watan Maris ya nufi Awe don ganawa da Sarki mai murabus.

KU KARANTA: Jami’an tsaro guda 40 ne suke tsaron tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi a Nassarawa

El-Rufai ya kai ma Malam Muhammadu Sunusi II ziyara a Awe

El-Rufai a kan hanyar zuwa Awe
Source: Facebook

Sai dai majiyar Legit.ng ta bayyana cewa duk kokarin da ta yi na jin ta bakin hadimin gwamnan a kan harkar watsa labaru, Ibrahim Musa, don jin ta bakinsa game da ziyarar ya ci tura, saboda wayoyinsa a kashe suke.

Haka zalika majiyar tsaron bata tabbatar da lokacin da El-Rufai zai koma jahar Kaduna ba. Idan za’a tuna a ranar Laraba ne El-Rufai ya nada Malam Muhammadu Sunusi a matsayin uban jami’ar jahar Kaduna, KASU.

Wannan nadi ya biyo bayan nadin da gwamnatin jahar Kaduna ta yi ma Sunusi a ranar Talata, 10 ga watan Maris ne inda ta nada shi mukamin mataimakin kwamitin gudanarwa na hukumar zuba hannun jari a jahar Kaduna.

A wani labari kuma, a ranar Laraba, 11 ga watan Maris cewa an kara adadin jami’an tsaron dake tsare da tsohon Sarki mai murabus a gidan da yake zaman hijira a garin Awe na jahar Nassarawa.

Daga cikin jami’an hukumomin tsaro da suka mamaye gidan da ake tsare da Sunusi a Awe akwai Yansanda, jami’an Civil Defence, da kuma na hukumar leken asiri, DSS, wanda suke ta karar duk wanda ya nufo gidan da nufin ganin Sarkin.

Daga cikin wadanda jami’an suka hana ganin tsohon sarkin akwai manyan sarakuna guda biyu da suka hada da Yakanajin Uke, Alhaji Ahmad Abdullahi da kuma Sarkin Karshi, Dakta Muhammad Bako.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel