Zargin karbar naira miliyan 300: Goodluck Jonathan ya karyata jam’iyyar APC

Zargin karbar naira miliyan 300: Goodluck Jonathan ya karyata jam’iyyar APC

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya musanta karbar kyautar naira miliyan 300 daga hannun jam’iyyar APC reshen jahar Bayelsa da tsohon zababben gwamnan jahar na APC, David Lyon wanda kotu ta soke nasararsa.

Jonathan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, inda yake mayar da martani ga wani kungiyar siyasa mai suna APC Reformation Forum wanda ta yi zargin Lyon ya baiwa Jonathan miliyan 300 da mota a shirye shiryen rantsar da shi gwamna domin ya kula da bakinsa.

KU KARANTA: Mutuwa ta yi awon gaba da hadiman gwamna guda 3 cikin kwanaki 5

“Wannan labari na kanzon kurege da APC Reformation Forum dake danganta kanta da jam’iyyar APC take yada shi a kafafen sadarwar zamani ba shi da tushe balle makama. Kungiyar na zargin David Lyon ya bayar da wadannan kudade ne ga Jonathan domin ya kula da bakin da ya gayyata zuwa nadin sa, ba komai bane illa zuki ta malle.

“Labarin nan cin mutunci ne ga kimar tsohon shugaban kasa Jonathan, saboda tun da farko babu wata bukatar APC ko wani ya baiwa Jonathan kudi da mota wai don ya halarci bikin nadin gwamna, bikin nadin da ba da shi aka shirya shi ba.

“Don haka muke shaida ma duniya cewa babu wata mota da APC baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, idan kuma akwai wanda ke da masaniya game da motar sai ya fallasa takardunta.” Inji shi.

Daga karshe Jonathan ya bayyana cewa an gudanar da zaben Bayelsa a akwatunan zabe da kuma kotuna, don haka lokacin cece kuce ya wuce, kamata yayi jama’a su rungumi kaddara su jira lokaci na gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel