Dalibi ya mance takardunsa a gida, iyayensa sun dauko jirgin sama sun kawo masa takardun makaranta sun koma gida

Dalibi ya mance takardunsa a gida, iyayensa sun dauko jirgin sama sun kawo masa takardun makaranta sun koma gida

- Masu karin magana suka ce wai kudi masu gidan rana, kwarai kuwa wannan magana haka take

- Domin kuwa wannan dalibin ya nuna yadda kudi suke da matukar muhimmanci, yayin da jawo kowa yake maganar shi a shafukan sadarwa

- Dalibin ya manta jakar makarantar shi ne a gida, sai iyayenshi suka dauko jirgin sama suka kawo masa ita suka koma abinsu

Wani bidiyo da yake ta faman yawo a shafukan sadarwa wanda ya nuna wasu iyayen wani dalibi masu kudi da suka dauki jirgi mai saukar ungulu suka nufi makarantar da yaron yake kawai domin su kai masa littafi da ya manta dashi a gida.

Wani mai amfani da dandalin Twitter mai suna Ituh Mokhele, shine ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa, inda mabiyansa suka cika da mamaki matuka.

Mutane sun yi ta faman addu'ar ina ma sune suke da irin wannan arziki, inda wasu kuma suke cewa suna son wannan mutane su dauki nauyinsu matukar zasu yadda.

"Dalibi ya manta jakar makarantar shi a gida, iyayen shi kuma suka dauko jirgin sama dungurungum domin su kawo masa jakar makaranta," Ituh ya rubuta.

A bidiyon, an gano wani saurayi da yake tafiya sanye da kayan makaranta zuwa wajen jirgin mai saukar ungulu, inda ya karbi jakar makarantar ya wuce abin shi.

Wanda ya dauki bidiyon an jiyo shi yana tambaya yana cewa, shin wanene wannan?

Bayan ya karbi wannan jaka saurayin ya wuce abinsa da kanshi sunkuye a kasa, saboda baya so ya jawo hankalin mutane kanshi.

Jirgin kuwa ya tashi ya wuce abin shi, amma 'yan kallo sun kasa daina mamakin wannan abu da ya faru a wajen.

'Yan kallon sun yi kokarin su tambayi saurayin ko shi wanene, da kuma su wanene iyayenshi, amma bai tsaya ya saurare su ba. Kawai ya jefa jakar shi a baya ya wuce abin shi ba tare da ya kula su ba.

Wannan bidiyo dai ya jawo hankalin mutane da dama, inda kimanin mutane dubu 100 suka kalli bidiyon, cikin mamaki.

Wasu sun ce akwai yiwuwar yaron ana takura mishi ne a makarantar shine ya sanya zai nuna musu ko shi wanene.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng