An kwashe littafai na kimanin N200m daga dakin karatun Sanusi II - Abba

An kwashe littafai na kimanin N200m daga dakin karatun Sanusi II - Abba

An kwashe a kalla litaffai da wasu takardu kimanin 40,000 daga katafaren dakin karatu na tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga fada zuwa wani wurin ajiya don adana su.

An cire Sanusi daga karagar mulki ne a ranar Litinin bayan an cimma matsayar aiwatar da hakan a zaman majalisar zartarwa na jihar Kano.

Babban sakataren sarkin, Mujtaba Abba ya ce an kai takardun wani wuri a jihar domin adana su a hirar da ya yi da Daily Nigerian.

An kwashe littafai na kimanin N200m daga dakin karatun Sanusi II - Abba

An kwashe littafai na kimanin N200m daga dakin karatun Sanusi II - Abba
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sanusi: Ganduje ya yi martani ga Kwankwaso a kan zargin sa hannun Buhari

Abba wanda bai dade da yin murabus ba daga sarautarsa na Falakin Kano ya ce, "Babban abinda mai martaba ya fi damuwa da su takardunsa ne, shi yasa ni da 'yar uwa ta muka tsaya domin mu tabbatar mun kwashe takardun. Mun shafe dare biyu ba mu barci kafin mu gama aikin."

Ya kuma bayyana kudin litaffan ya dara naira miliyan 200.

Ya ce, "Ni ne na yi cinikin mafi yawan littafan kuma ina fada maka a ban cika ba ma a kalla kudinsa ya fi naira miliyan 200."

Game da dawakansa kuma, ya ce: "A cikin kyawawan dawakansa da suka fi 40 da siddi 100, ya dauki doki daya tak da sidi daya sauran kuma ya bar wa magajinsa."

A wani rahoton, kun ji cewa an canja wa tsohon sarkin Kano, Sanusi II masauki daga Loko zuwa Awe bayan ya kwana daya a Loko.

Hakan ya faru ne bayan sarkin garin na Loko ya bukaci a canja wa Sanusi gari domin babu isasun ababen more rayuwa kamar lantarki a garin kuma a cewarsa ba dai-dai bane babban mutum kaman Sanusi ya zauna ba na'urar sanyaya daki wato AC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel