Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zubar da hawaye yayin karbar takardar kama aiki

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zubar da hawaye yayin karbar takardar kama aiki

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zubar da hawaye a ranar Laraba jim kadan bayan ya karbi takardar kama aikinsa daga wurin Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano.

Bayero, wanda kafin ranar Litinin shine sarkin Bichi, ya shaidawa mutanen tsohuwar masarautarsa cewa Allah ne ya kaddara cewa zai bar su ya koma wata masarautar.

Sarkin ya ce, "Zan bar ku ba domin bana son zama tare da ku ba. Haka Allah ya kaddara mana baki daya."

A jawabinsa, Ado Bayero wanda ya zama sarkin Kano bayan cire Muhammadu Sanusi II ya ce mahaifinsa ya musu tarbiyya cewa su rika girmama manya.

Ya yi alkawarin biyayya ga gwamnatin Abdullahi Ganduje, gwamnan Kano da kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zubar da hawaye yayin karbar takardar kama aiki
Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zubar da hawaye yayin karbar takardar kama aiki
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sanusi: Ganduje ya yi martani ga Kwankwaso a kan zargin sa hannun Buhari

"Mun yi imanin komi yana da karshe. Dole mu tuna da tsohon sarkin mu Ado Bayero da ya koyar da mu cigaba da imani da Allah. Ya kuma bamu tarbiyyar cewa mu rika yi wa manya biyayya," in ji shi.

"Ya tabbatar mana da cewa hakuri ne kai samar da nasara. Yanzu mun gani a hakika darasin da ya koyar da mu. Ina horar da ku ku zama masu imani da Allah tare da kyautata wa junan ku domin kawo cigaba a masarautar Kano da Najeriya baki daya."

Sabon sarkin ya kuma mika godiyarsa ga masu nadin sarki su hudu don zaben sa da suka yi, ya kuma yi alkawarin zai cigaba kiyaye kima da darajar masarautar da aka kafa shekaru 200 da suka gabata.

Da ya ke nasa jawabin, sabon sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya yi wa Allah godiya da ya nada shi sarki.

Ya ce, "Muna gode wa Allah da ayyukan da magabatan mu suka yi. Muna kuma addu'a Allah yasa suna cikin ni'imarsa. Muna addu'a Allah ya hada kan mu baki daya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel