Yadda rikicin Sanusi da Ganduje ya samo asali shekaru 3 da suka gabata - Hadimin Ganduje
Salihu Yakasai, mai taimakawa Gwamna Umar Ganduje na musamman a kan kafafen watsa labarai ya bayar da labarin yadda rikici tsakanin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Ganduje ta samo asali.
Ya yi wannan jawabin ne yayin wata shiri da aka yi a Silverbird Television kamar yadda The Punch ta ruwaito.
A cewar Yakasai, rikici tsakanin Sanusi da gwamnan ya samo asali ne shekaru uku da suka gabata.
Ya ce rikicin ya yi zafi ne lokacin da tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya ya soki Ganduje a wurin wani taro a Kaduna.
Yakasai ya ce, "Bari in fara daga farko tun kimanin shekaru uku da suka gabata. Wannan shine asalin rikicin. Lokacin da tsohon sarkin ya soki gwamna kuma ya kunyata shi a bainar jama'a a Kaduna a kan batun jiragen kasa na zirga-zirga a gari.

Asali: Instagram
DUBA WANNAN: Kauyen Loko: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata a sani game da masaukin Sanusi na farko
"A kan batun, Sarkin yana da damar ya gana da gwamna kuma gwamna ya saurare shi domin ya fada wa gwamna ra'ayinsa a kan aikin jirgin kasar.
"Amma a maimakon ya yi hakan sai ya bari suka tafi wurin taro da aka dauka a talabijin ya soki gwamnan. Tun daga lokacin, dangantaka tsakaninsu ta cigaba da tabarbarewa.
"Bayan kirkiran sabbin masarautu, za kayi tsammanin Sarki Sanusi zai bari komai ya wuce tunda kotu ta tabbatar cewa an bi ka'ida wurin kirkiran masarautun. Tun daga lokacin, Sarkin ya fara janye wa daga hallarton taron gwamnati wanda hakan wajabi ne a kansa. Ba kuma ya tura wakilai.
"Mun yi wani taro mai muhimmanci lokacin da muka kaddamar da ilimi kyauta a Kano na sakandare tare da shirin saka almajirai cikin harkar makarantun boko wanda a lokacin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo ya hallarta. Taron na da matkukar muhimmanci ga jihar, ministoci da wakilan kasashe da mambobin kungiyoyi na kasashen duniya sun hallarci taron. Sarkin yana Kano amma bai hallarci taron mai muhimmanci ba.
"Saboda haka abin akwai daure kai idan ka lura cewa gwamnati na kokarin aiwatar da ayyukan inganta rayuwa al'umma amma Sanusi ba zai zo ya bayar da gudunmawarsa ba na karfafawa gwamnati gwiwa. Dukkan wadandan da wasu abubuwan da ba za mu iya fada ba ne suka janyo abinda ya faru."
Ya kara da cewa Ganduje ya yi hakuri wurin mu'amulantar Sanusi.
Hadimin gwamnan ya kuma zargi Sanusi da mara wa jam'iyyar PDP baya a zaben gwamna na 2019 da aka gudanar a jihar.
Ya ce, "Babu wanda zai nade hannunsa yana kallon ana masa haka. Gwamnan ya yi hakuri da Sanusi na tsawon shekaru hudu."
Ya kuma ce duk taron sulhun da aka yi ba su yi nasara ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng