Rikici ya barke wajen rabon gado bayan matar mamacin ta gano cewa mijinta yayi auren sirri kafin ya mutu

Rikici ya barke wajen rabon gado bayan matar mamacin ta gano cewa mijinta yayi auren sirri kafin ya mutu

- Robert Ngundo da Zipporah Moraa sunyi aure na tsawon shekaru 11

- Ngundo yayi aikin soja sannan ya mutu a watan Disambar shekarar 2013 a Entebbe, kasar Uganda

- Moraa ta sanar da kotun Nakuru cewa ta gano mijinta ya auri wata mata mai suna Elizabeth Mutinda ba tare da saninta ba

Wata bazawara mai shekaru 52 ta gano cewa mijinta wanda ya mutu yana da wata matar daban da ita ba ta sani ba, inda hakan ya sanya rikicin dukiyar mamacin.

Zipporah Moraa ta gano cewa mijin nata na cin amanarta bayan wata jarida data bayyana rahoton mutuwarsa ta bayyana duka sirrinsa.

Ta sanarwa da kotun Nakuru cewa ta gano wata mata mai suna Elizabeth Mutinda ta auri mijinta, bayan rahoton da jaridar da ruwaito rasuwar tayi.

A wani rahoto da The Standard ta fitar a ranar 10 ga watan Maris dinnan ta bayyanawa alkalin kotun Justice Rachel Ng'etich cewa mijinta ya bar ta cikin duhu akan maganar dayar matar tashi saboda ita bai taba yi mata zancenta ba tsawon shekaru 11 da suka kwashe suna tare.

Ngundo tsohon soja ne a kasar ta Uganda, inda ya mutu yana da shekaru 48 a duniya a shekarar 2013, a lokacin da yake kan hanyarshi ta dawowa daga filin daga a kasar Sudan.

KU KARANTA: Wani kare da baya iya tafiya ya fara kawance da wata tattabara da ba ta iya tashi

A bayanin da Moraa ta yiwa kotu, ta bayyana cewa mutuwar mijinta ba karamin tashin hankali ta zama a gareta ba, saboda ko wajen binneshi an hana ta zuwa, yanzu kuma gashi ta gano cewa yana da wata matar ma.

Mora ta ce lokacin da ta nemi a bata kimanin naira miliyan uku domin ta biyawa yaranta guda uku kudin makaranta, ta gano cewa kishiyarta taje kotu ta hana a bata kudin wanda mijin nasu ya mutu ya bari.

Matar da ake rikicin a kanta dai ta bayyanawa kotu hadda takardun aurensu da tsohon sojan.

Yanzu dai alkalin kotun ya dage sauraron karar har zuwa ranar Litinin 8 ga watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel