An tsaurara tsaro a sabon gidan Muhammadu Sanusi II da ke Awe

An tsaurara tsaro a sabon gidan Muhammadu Sanusi II da ke Awe

- Jami’an tsaro sun kewaye gidan da aka ajiye tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a garin Awe

- Sarkin Kanon na tare da Baffansa, Dan Buran Kano, Munir Sanusi, wanda ya kasance Shugaban ma’aikatan Sanusi a lokacin da ya ke kan gadon sarauta

- Sanusi dai na zaune ne a gidan Shugaban karamar hukumar Awe, a jahar Nasarawa

Rahotanni da muke samu a yanzu sun nuna cewa an zuba jami’an tsaro kewaye da gidan da aka ajiye tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi wanda gwamnatin jahar karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta tsige.

A yanzu haka dai Muhammadu Sanusi na zaune ne a gidan Shugaban karamar hukumar Awe, a jahar Nasarawa.

An tsaurara tsaro a sabon gidan Muhammadu Sanusi II da ke Awe
An tsaurara tsaro a sabon gidan Muhammadu Sanusi II da ke Awe
Asali: Facebook

Har ila yau mun ji cewa tsohon sarkin Kanon na tare da Baffansa, Dan Buran Kano, Munir Sanusi, wanda ya kasance Shugaban ma’aikatan Sanusi a lokacin da ya ke kan gadon sarauta.

A baya mun ji cewa korarren sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya dauki alwashin shigar da gwamnatin jahar Kano gaban kotu biyo bayan tsige shi da ya yi daga mukamin Sarautar Kano, tare da garkame shi.

KU KARANTA KUMA: Ba mu kori Sanusi daga Kano ba – Gwamnatin Ganduje

Lauyan Sanusi, Abubakar Mahmoud SAN ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, inda yace Sunusi ya basu umarnin kalubalantar tsige shi da aka yi, da kuma garkame shi da aka yi.

A cewar Mahmoud, garkame Sarki a wani wuri tare da hana shi walwala ba shi da asali a kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ya yi kira ga gwamnatin Kano ta sakan masa mara ya yi fitsari cikin sa’o’I 24 ko kuma ya kai shi kotu.

“Sakamakon umarnin tsohon Sarki ta hannun babban hadiminsa, ya bamu daman shigar da karar gwamnati gaban kotu domin kalubalantar tsige garkame shi tare da fatattakarsa daga garin Kano, muna da tabbacin hakan ya saba ma sashi na 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya daya baiwa kowa daman walwala."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel